Home Back

Taken Najeriya: Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Muhimmiyar Dokar da Majalisa Ta Zartar

legit.ng 2024/7/3
  • Daga wannan ranar ta 29 ga watan Mayun 2024, Najeriya ta daina amfani da taken kasa na “Ku tashi, ya ku ‘yan kasa”
  • Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu a kan dokar dawo amfani da tsohuwar wakar taken kasar ta “Nigeria, mun jinjina miki”
  • A shekarar 1978 ne sojoji suka soke amfani da tsohon taken kasar, bayan shekaru 46 kuma Shugaba Bola Tinubu ya dawo da shi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu a kan kudirin dokar taken Najeriya da majalisar dokokin kasar ta zartar a ranar Talata.

Da wannan dokar da Shugaba Tinubu ya amince da ita a yau Laraba, za a dawo amfani da tsohuwar wakar taken kasar ta “Nigeria, mun jinjina miki”.

Tinubu ya rattaba hannu kan dokar taken Najeriya
Tinubu ya sa hannu kan dokar komawa amfani da tsohon taken Najeriya. Hoto: @HouseNGR Asali: Twitter

A shekarar 1978 ne sojoji suka soke amfani da tsohon taken kasar, bayan shekaru 46 kuma Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar dawo da taken, in ji rahoton Arise TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya amince da dokar taken Najeriya

Shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio, a wani zama na hadin guiwa na majalisar tarayya ya ce Tinubu ya ratta hannu kan kudurin dokar kuma zai kaddamar da taken.

Channels TV ta ruwaito Tinubu ya tabbatar da komawa amfani da taken ‘'Nigeria, mun jinjina miki'’ maimakon taken “Ku tashi, ya ku ‘yan kasa” a zaman taron hadin gwiwa na majalisar.

A baya mun ruwaito majalisar dattawa da ta wakilai sun amince da dokar sauya taken kasar daga a wasu zaman majalisar daban-daban.

Yadda ake rera sabon taken Najeriya

Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fuskar kafofin sada zumunta, Bashir Ahmad ya wallafa taken da za a rika amfani da shi yanzu a shafinsa na X.

Asali: Legit.ng

People are also reading