Home Back

Ana Tsaka da Rikicin Sarautar Kano, Jam'iyyar Kwankwaso Ta Aike da Saƙo Ga Bola Tinubu

legit.ng 2024/7/1
  • Jam'iyyar NNPP mai kayan maramari ta yabawa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a lokacin da yake cika shekara ɗaya a mulki
  • Uban NNPP Boniface Aniebonam ya ce tun asali Bola Tinubu ya karɓi kasar a lokacin da matsaloli suka mata katutu
  • Ya bukaci shugaban kasa ya naɗa mutanen kirki a nuhimnan wurare domin aiwatar da manufar sabunta fata da kawo ci gaba a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - New Nigeria People’s Party (NNPP) ta yabawa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu yayin da yake murnar cika shekara guda a kan madafun iko.

Uban jam'iyyar NNPP, Dokta Boniface Aniebonam, ya ce shugaban ƙasa ya san ƙalubalen da kasar nan ke fuskanta a lokacin ya karɓi mulki bara.

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Uban NNPP ya yabawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Asali: Facebook

Ya bayyana haka ne yayin wata hira da hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) game da cikar gwamnatin Tinubu shekara ɗaya ranar 29 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Daily Trust ta kawo, ya ce ganin irin kalubalen da al’ummar kasar ke fuskanta ne ya sanya shugaban kasar ya fito da ajandar sabunta fata domin tunkarar matsalolin.

"Shugaba Tinubu mutum ne kamar kowa, ta yiwu akwai wuraren da ya yi kuskure kamar cire tallafin man fetur ba tare da tsara yadda za a magance tasirin ba, amna karshe dai zai zama alheri.

"Don haka wannan lokaci ne da ya kamata ‘yan Nijeriya su kara azama wajen yin aiki tukuru da sadaukarwa domin ci gaban kasarmu."

- In ji Dakta Boniface Aniebonam.

A cewar Aniebonam, Tinubu da ‘yan tawagarsa sun yi nasarar ceto Najeriya daga sashin kula da waɗanda suka kai gargara, ya dawo da ita cikin hayyacinta.

Ya bukaci shugaban kasar da ya tabbatar ya zaƙulo kwararrun mutane ya naɗa su a muhimman wurare don tafiyar da tsarin sabunta fata domin ci gaban Najeriya.

Uban NNPP ya ce ya kamata Tinubu ya tabbatar da cewa manyan titunan ƙasar nan na cikin yanayi mai kyau don rage hadurra da sace-sacen mutane da sauran laifuka.

Gwamnatin Jigawa ta ɗauki ma'aikata

A wani rahoton kuma Gwamna Umar Namadi ya ce gwamnatinsa ta ɗauki sababbinmalamai domin cike giɓin da ke akwai a ɓangaren ilimi a jihar Jigawa

Namadi ya ce ilimi na ɗaya daga cikin manufofi 12 da gwamnatinsa ta sa a gaba da nufin ɗaga darajar jihar ta ƙara ɗaukaka

Asali: Legit.ng

People are also reading