Home Back

Zaben Gwamna: APC Ta Rasa Babban Jigon da Take Ji da Shi, Ya Samu Matsayi a NNPP

legit.ng 2024/7/3
  • Barista Olugbenga Edema ya zama ɗan takarar gwamnan jihar Ondo a inuwar NNPP bayan ya baro All Progressives Congress (APC)
  • Tsohon jigon jam'iyya mai mulki ya ce ya shirya sauke Gwamna Lucky Aiyedatiwa daga mulki a zaɓen watan Nuwamba, 2024
  • NNPP ta bai wa Edema tikitin takara ne bayan tsohon ɗan takararta, Oluwatosin ya janye daga takara bisa ra'ayin kansa da kishin jam'iyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Barista Olugbenga Edema, ɗaya daga cikin manyan ƴan takara da suka nemi tikitin takarar gwamna a jihar Ondo ya koma New Nigeria People’s Party (NNPP).

Jim kaɗan bayan haka NNPP ta miƙawa Barista Edema tikitin takarar gwamna a zaɓen gwamnan Ondo da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamba, 2024.

Jam'iyyar NNPP.
Jam'iyyar NNPP ta sake tsayar da ɗan takarar gwamna a jihar Ondo Hoto: New Nigeria People’s Party (NNPP) Asali: Twitter

Edema ya zama ɗan takarar NNPP ne a zaɓen fitar da gwani da jam'iyyar ta shirya a Akure, babban birnin jihar Ondo ranar Laraba, jaridar Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An shirya zaben ne domin maye gurbin tsohon ɗan takarar gwamna, Ayeni Oluwatosin, wanda ya janye haka kurum.

Barista Edema ya bugi ƙirjin cewa ya shirya kayar da da ɗan takarar APC kuma gwamna mai ci, Lucky Aiyedatiwa idan a akwatun zaɓe.

Meyasa ɗan takarar NNPP ya janye?

A wasiƙar da ya miƙa domin tabbatar da janyewarsa daga takara, Mista Oluwatosin ya ce ya ɗauki matakin ne domin ɗaga ƙimar NNPP.

“Ni, Ayeni, Oluwatosin Israel, dan takarar gwamna a NNPP a zaben da za a yi ranar 16 ga Nuwamba, 2024 a jihar Ondo, na haƙura da takara.

"Ba don komai na janye daga takara ba sai don ina kishin jam'iyyata NNPP," in ji shi.

Haka nan kuma Mista Peter Olagookun, shugaban NNPP na jiha Ondo ya tabbatar da janyewar dan takarar, kamar rahoton Vanguard ya kawo.

Ya ce babu wanda ya tilasta masa, ya janye ne bisa ra'ayin kansa kuma domin ya ba NNPP damar zaƙulo ɗan takarar da zai baiwa maraɗa kunya.

Atiku ya ce tallafin mai ya dawo

A wani rahoton kuma Atiku Abubakar ya buƙaci shugaban ƙasa ya fito ya faɗawa ƴan Najeriya gaskiya game da biyan tallafin man fetur a gwamnatinsa.

Wazirin Adamawa ya yi ikirarin cewa cire tallafi duk maganar baka ce, inda ya ce kuɗin tallafin bana 2024 ka iya kai wa N5.4trn.

Asali: Legit.ng

People are also reading