Auren Jinsi: Dan Majalisar Kano Na Neman Najeriya Ta Sa Hannu Kan Yarjejeniyar Samoa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Sumaila/Takai a Kano, Rabiu Yusuf ya ce Najeriya na iya amincewa da sassa masu kyau na yarjejeniyar Samoa.
Hon. Yusuf ya ce yarjejeniyar ta kasance abu mai wahala da za a iya tattaunawa a kai saboda tana kunshe da wani bangare na mutunta 'yancin auren jinsi.
Jaridar The Cable ta ruwaito yarjejeniyar Samoa wani babban tsarin doka ne na karfafa dangantaka tsakanin kasashen kungiyar Afirka, Caribbean, da Pacific (OACPS) da kuma Tarayyar Turai (EU).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kasashen da ke cikin yarjejeniyar sun hada da kasashen Afirka 47, ciki har da Najeriya, 16 daga yankin Caribbean, kasashe 15 na Pacific, da kuma Jamhuriyar Maldives.
An yi imanin cewa yarjejeniyar Samoa tana goyon baya da kuma kare haƙƙin 'yan luwadi, 'yan madigo, masu canza jinsi, da sauran halayen jima'i da ba na al'ada ba, rahoton BusinessDay.
Sai dai Najeriya ta fice daga rattaba hannu kan yarjejeniyar a watan Nuwambar bara bayan da wasu kungiyoyin farar hula suka nuna damuwa game da sashe na 9 na yarjejeniyar.
Hon. Yusuf ya bayyana ra'ayinsa dangane da yarjejeniyar Samoa a ranar Alhamis yayin wani taron yanar gizo da cibiyar habaka aikin jarida (CJID).
Dan majalisar wakilan ya lura cewa yarjejeniyar Samoa tana da fa'ida ga Najeriya, don haka akwai bukatar a dauki kasadar amincewa da ita amma a kafa sharadi.
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Kano ta yi martani kan hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke game da shari'ar dokar rusa masarautun jihar.
Kwanishinan shari'a na Kano, Barista Haruna Isah Dederi ya ce har yanzu Muhammadu Sanusi II ne sarkin Kano bisa ga bayanin wannan hukunci na kotun.
Asali: Legit.ng