Home Back

Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da ƙasar Falasɗinu

premiumtimesng.com 2024/5/23
Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da ƙasar Falasɗinu

Majalisar Ɗinkin Duniya ta kaɗa ƙuri’ar amincewa ƙasar Falasɗinu zama cikakkar mamba a cikin majalisar.

Majalisar ta kuma yi kira ga Majalisar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince Falasɗinu ta zama ƙasa ta 194 a jerin mambobin Majalisar Ɗinkin Duniya (UN).

A ranar Juma’a ce ƙasashe 194 suka jefa ƙuri’ar, wanda yunƙuri ne na amincewa da ƙasar Falasɗinu, bayan Amirka ya ƙi amincewa a watan da ya gabata.

Ƙasashe 143 ne daga cikin 193 suka amince, sai 9 ba su amince ba.

Waɗanda ba su nuna goyon bayan su ba, sun haɗa da Amurka da Isra’ila. Sai ƙasashe 25 da suka ƙi jefa ƙuri’ar amincewa ko rashin amincewar su.

A Afrika, Najeriya da sauran ƙasashe duk sun kaɗa ƙuri’un amincewa, in banda ƙasar Malawi, wadda ba ta zaɓi goyon baya ko rashin goyon ba.

Dama ko a cikin Disamba sai da Malawi ta ƙaurace wa zaɓen tilasta Isra’ila tsagaita wuta a yaƙin Falasɗinu.

Ƙasashe da dama waɗanda suka goyi bayan amincewa da ƙasar Falasɗinu, sun haƙƙaƙe cewa sun yi ne don samun ‘yanci da kare fararen hula, musamman mata da ƙananan yara, sai kuma ‘yancin ɗan Adam a Gaza.

Ƙuri’un da aka kaɗa ranar Juma’a ba za su bai wa Falasɗinu zama cikakkar mamba ba, amma za a amince da ita cewa ta cancanci zama mamba.

Falasɗinu na buƙatar amincewar Majalisar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya tukunna.

People are also reading