Home Back

Shehun Borno Ya Bukaci Tinubu Ya Kwato Kananan Hukumomin Da Ke Hannun ‘Yan Boko Haram

leadership.ng 2024/7/1
Shehun Borno Ya Bukaci Tinubu Ya Kwato Kananan Hukumomin Da Ke Hannun ‘Yan Boko Haram

Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar-Ibn Garbai Al-Amin El-Kanemi, ya yi kira ga Shugaban kasa, Bola Tinubu da hukumomin tsaro da su tabbatar da yin duk mai yiyuwa wajen kawar da sauran ‘yan ta’addan Boko Haram da har yanzu suke rike da shalkwatar karamar hukumar Guzamala da wasu kauyuka da ke Kukawa, karamar hukumar Abadam, domin bai wa miliyoyin mazauna yankunan da suka yi gudun hijira damar komawa gidajensu na asali.

Shehun Borno ya kuma lura da cewa hanya daya tilo da za a samu dawo da karfin ikon mulkin farar hula a wadannan yankunan da abun ya shafa shi ne, hukumomin tsaro su tashi tsaye su gwabza yaki da ‘yan ta’addan har sai sun amshe iko da yankunan daga hannunsu, musamman a karamar hukumar Guzamala, inda babu wani farin hulan da ke wajen tsawon shekaru.

Basaraken ya shaida hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar barka da sallah ga mai rikon mukamin gwamnan Jihar Borno, Dakta Umar Kadafur a gidan gwamnatin jihar da ke Maiduguri a ranar Lahadi.

LEADERSHIP ta labarto cewa irin wannan rokon ya kuma fito daga bakin kakakin majalisar dokokin Jihar Borno, Hon. Abdulkarim Lawan a lokacin da ke gabatar da sakonsa na ranar tunawa da samun ‘yancin kan Nijeriya na 2024.

Shehun a daidai lokacin da ke yaba wa kokari da sadaukarwar sojojin Nijeriya wajen dawo da martabar zaman lafiya a shiyyar arewa maso gabas da ma Nijeriya baki daya, ya ce, gazawar sojojin kuma wajen kwato yankunan da ke hannun ‘yan Boko Haram ya zama babban damuwa ga iyaye da dama na hanasu zuwa gonakansu da ba su damar nema wa ‘ya’yansu ilimi mai inganci da suke da burin samu. Ya misalta hakan a matsayin babban kalubalen da zai iya kawo cikas ga ci gaban da ake has ashen samu.

Sarkin ya ce, “Na zo nan ne ni da mutanena domin taya gwamnati da al’umman Jihar Borno murnar gudanar da shagurgulan babban sallah cikin kwanciyar hankali.

“Ina yaba wa gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro, musamman gwamnan Babagana Zulum bisa kokarinsu da suke yi wajen ganin sun yaki ‘yan ta’addan Boko Haram.

“Bugu da kari, bari na yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga Shugaban kasa Bola Tinubu da hukumomin tsaro da su tashi tsaye wajen kawar da ‘yan ta’addan Boko Haram da suka mayaye shalkwatar karamar hukumar Guzamala, da wasu kauyuka da ke Kukawa, karamar hukumar Abadam domin ganin an samu yanayin da miliyoyin mazauna yankunan za su samu damar komawa gidajensu,” Shehun Borno ya shaida.

Da yake maida jawabi, mai rikon gwamnan jihar, Dakta Kadafur, ya gode wa sarkin bisa wannan ziyarar barka da sallah.

Ya ce tuni aka kafa kwamiti a karkashin jagorancin kwamishinan kula da kananan hukumomi da harkokin masarautu, Hon. Sugum Mai Mele, ya kuma ce gamayyar jami’ar tsaro (MNJTF) suna aiki tukuru wajen ganin sun tabbatar komai ya dawo yadda yake tare da tabbatar da cewa mutanen da suka bar gidajensu a Guzamala sun samu damar komawa gidajensu na asali.

Ya tabbatar da cewa kafin karewar wa’adin gwamnati mai ci kowani dan gudun hijira zai koma gidansa na asali.

People are also reading