Home Back

Gwamnatin Kano ta Gano Yadda Miliyoyin Dalibai ke Zama a Kasa, an Cefanar da Makarantu

legit.ng 2024/7/1
  • Gwamnatin Kano ta bayyana cewa an samu tabarbarewar gaske a sashen ilimin jihar domin akalla dalibai miliyan 4.7 ne ke zaune a kasa saboda rashin kujeru a ajujuwansu a makarantu
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya bayyana haka ya nuna takaici matuka kan yadda ake samun Karin yara marasa zuwa makaranta da kididdiga ta nuna yanzu haka sun haura miliyan 1
  • Gwamnan ya ce akwai matsaloli kamar rashin kwararrun malamai, kuma zai hada kai da kungiyar malamai domin gano sauran matsalolin sashen ilimi da zumar warware su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoGwamnatin Kano ta zargi tsohuwar gwamnatin da gazawa wajen inganta ilimi bayan ta samu dalibai miliyan 4.7 na zama a kasa babu kujeru a ajujuwansu a fadin makarantun jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya yi zargin, inda ya kara da cewa an sayar wasu daga makarantun jihar, wasu kuma an mayar da su na amfanin kashin kai.

Gwamna
Gwamnatin Kano ta gano daliban miliyan 4.7 da ke zaune a kasa babu kujeru Hoto: Abba Kabir Yusuf Asali: Twitter

Daily Trust ta wallafa yadda gwamnan ya shiga takaicin karuwar yara marasa zuwa makaranta, yayin da aka yi kiyasin yara sama da miliyan daya ne ba su zuwa makaranta duk da sun a cikin shekarun zuwa din.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Mun dauki matakin gyara ilimi,” Abba

Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnati ta bayyana kan bangaren ilimi da zummar daukar matakan kawo gyara da inganta fannin saboda rayuwar yaran Kano ta yi kyau.

Ya ce gwamnati za ta yi aiki da kungiyar malamai ta kasa (NUT) domin samun hanyoyin warware matsalolin da su ka dabaibaye sashen ilimi a Kano, kamar yadda Vanguard News ta wallafa.

Daga matsalolin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce bangaren ilimin jiharsa na fuskanta akwai rashin wadatattun kuma kwararrun malamai, rashin kayan aiki da kuma aiki da tsofaffin kayan koyo da koyarwa.

Sauran matsalolin sun hada da rashin tsaftaaccen ruwa ko rashin Ruwan baki dayansa a makarantun gwamnatin Kano.

An sanya dokar ta baci kan ilimi

A wani labarin kun ji cewa gwamnatin Kano ta ayyana dokar ta baci a kan sashen ilimi a jihar domin inganta bangaren tare da daukar matakan kawo gyara cikin gaggawa.

Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa ne ya bayyana matakin a Dutsen jihar Jigawa, inda ya yi gargadin cewa ba za a sake sauya malami daga kauye zuwa birni ba saboda son zuciya.

Asali: Legit.ng

People are also reading