Home Back

Man City na son raba Musiala da Bayern, Arsenal na neman 'yan gaba ciki har da Olise

bbc.com 2024/5/3

Asalin hoton, Getty Images

Jamal Musiala
Bayanan hoto, Mahaifin Jamal Musiala, Bayarabe ne dan Ingila asalin Najeriya, mahaifiyarsa kuwa 'yar Jamus

Mintuna 2 da suka wuce

Dan wasan gaba na Bayern Munich Jamal Musiala na neman zama na farko da Manchester City ke son saye a bazara, amma kuma Chelsea ma na sa ido a kan dan wasan na tawagar Jamus. (Guardian)

Sai dai kuma Bayern ba ta da niyyar sayar da matashin dan wasan mai shekara 21, hasali ma tana shirin kulla sabuwar yarjejeniya da shi ne. (Fabrizio Romano)

Arsenal na duba yuwuwar samo dan wasan gaba mai kai hari da kuma dan gaba na gefe a bazara, kuma daga cikin wadanda take hari akwai Alexander Isak, na Newcastle, dan Sweden mai shekara 24 da kuma Micheal Olise, na Faransa mai shekara 22, wanda yake Crystal Palace. (Guardian)

Haka kuma Gunners din na sa ido a kan dan gaban RB Leipzig da Slovenia Benjamin Sesko, mai shekara 20. (Standard)

Ita ma Chelsea da kuma Manchester United na sa ido a kan Sesko, wanda yake da sharadin sayar da shi a kan yuro miliyan 50 a kwantiraginsa. (Ben Jacobs)

Besiktas na neman daukar mataimakin kociyan Liverpool Pep Lijnders, domin zama babban mai horad da 'yanwasanta, gurbin da a yanzu babu kowa. (Athletic )

Liverpool da Paris St-Germain, na duba yuwuwar sayen dan bayan Chelsea da Ingila Levi Colwill, mai shekara 21. (GiveMeSport)

Tottenham na son tsohon dan wasan gaba na Arsenal Serge Gnabry, kuma Bayern Munich na da niyyar sayar da dan wasan na tawagar Jamus. (Football Insider)

Haka kuma Spurs din, ita ce kan gaba a masu neman sayen dan wasan tsakiya na Nottingham Forest Morgan Gibbs-White, kuma a shirye kungiyar ta London take ta same dan Ingilar a bazara. (Football Insider)

Ana sa ran Romelu Lukaku ya koma Chelsea a karshen kakar nan daga zaman aron da yake yi a Roma, wadda ba za ta iya sayen dan wasan na Belgium ba a kan yuro miliyan 43 domin zama nata dindindin. (Gazzetta dello Sport )

Chelsea da Newcastle United na sha'awar sayen mai tsaron ragar Arsenal da Ingila Aaron Ramsdale, mai shekara 25. (CaughtOffside)

Wakilin Julian Nagelsmann ya ce, kociyan na Jamus yana tattaunawa da Bayern Munich domin karbar aikin horad da kungiyar, kuma a mako mai zuwa ne kila zai bayyana shawarar da ya yanke. (Spielmacher podcast daga Metro)

Tsohon kociyan Liverpool da Everton Rafael Benitez zai kama aiki da Sao Paulo, wata daya bayan Celta Vigo ta kore shi. (Sun)

People are also reading