Home Back

‘Yan Majalisar Wakilai Sun Buƙaci A Mayar Da Wa’adin Mulkin Nijeriya Falle Ɗaya Mai Shekaru 6

leadership.ng 2024/7/1
‘Yan Majalisar Wakilai Sun Buƙaci A Mayar Da Wa’adin Mulkin Nijeriya Falle Ɗaya Mai Shekaru 6

Wata Ƙungiya ‘yan Majalisar wakilan Nijeriya su 30 da aka fi sani da “Reform Minded Lawmakers” daga Jam’iyyun Siyasa daban-daban (G-30), sun bayar da shawarar mayar da wa’adin mulke ɗaya ga Shugaban kasa na shekara shida da sauran Kujerun Mulki na shiya 6 na faɗin Nijeriya, cikin jerin kudurori da suka gabatar a gaban majalisar.

‘Yan majalisar sun kuma bayar da shawarar yadda za a gudanar da zaben shugaban ƙasa da na majalisar tarayya da na gwamnoni da na majalisun jihohi da na kananan hukumomi har da birnin tarayya duk a rana daya.

‘Yan majalisar na “Reform Minded” sun bayyana hakan ne a lokacin da suke ganawa da manema labarai kan kudirori 50 da suka ɗauka, wadanda suka samu karatu na farko a zauren majalisar wakilan tarayya a Abuja ranar Litinin.

Da yake karanta jawabin a taron manema labarai, ɗaya daga cikin yan Majalisun kuma mamba mai wakiltar mazabar Ideato ta Arewa da Kudanci Jihar Imo, Ikenga Imo Ugochinyere, ya ce suna bayar da shawarar yin gyare-gyare a kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999, don samar da tsarin karba-karba na zartaswa a tsakanin shiyyoyi shida na siyasa da ke ƙasarnan da zummar tabbatar da daidaiton wakilci tare da rage matsananciyar damuwa da tashin hankali da ma ƙirƙiro sabbin jihohi a Nijeriya.

Ugochinyere ya kuma nemi a gyara kundin tsarin mulkin ƙasa domin samar da ofishin mataimakan shugaban kasa biyu daga yankin kudu da arewacin Nijeriya, inda mataimakin na daya zai kasance mataimakin shugaban kasa, shi kuma mataimakin na biyu zai kasance minista mai kula da tattalin arziki.

Ya ci gaba da cewa, ƙudirorin suna neman a yi wa kundin tsarin mulki gyara don ganin shugaban ƙasa da mataimakinsa na daya za su fito daga yanki daya na kasar nan (Arewa ko Kudu), kuma mataimakin shugaban ƙasa na daya zai zama shugaban ƙasa a duk lokacin da shugaban ƙasar ya gaza.

People are also reading