Home Back

Ana Tsaka da Ruɗanin Hukuncin Kotuna 2, Jigon NNPP Ya Yi Magana Kan Naɗin Sarkin Kano

legit.ng 2024/6/30
  • Yayin da rigimar sarauta ke kara ƙamari a Kano, jigon NNPP ya yaba da mayar da Muhammadu Sanusi kan karagar Sarkin Kano
  • Tsohon ɗan takarar gwamna a inuwar NNPP a jihar Ogun, Ambasada Olufemi Ajadi ya ce Kano za ta ƙara bunƙasa a karkashin Sarki Sanusi II
  • Ajadi ya yi kira ga sarki na 15, Aminu Ado Bayero da magoya bayansa su haƙura su bar zaman lafiya ya zauna kamar yadda aka saba a jihar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Wani jigo a New Nigeria People's Party (NNPP), Ambasada Olufemi Ajadi Oguntoyinbo, ya yaba da dawowar Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

Idan baku manta ba tsohuwar gwamnatin Kano karkashin Gwamna Abdullahi Ganduje ta sauke Sanusi II bayan majalisar dokoki ta kirkiro masarautu biyar.

Muhammadu Sanusi II
Jigon NNPP ya yaba da mayar da Sanusi II kan karamar sarautar Kano Hoto: Sanusi Lamido Sanusi Asali: Twitter

Kamar yadda Tribune Nigeria ta tattaro, Sanusi II ya koma kan karagar sarauta sanar Jumu'a da ta gabata bayan majalisar dokokin Kano ta rushe masarautun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu kan dokar da majalisar dokokin ta sabunta a wani taro da ya samu halartar manyan jami'an gwamnatin Kano ranar Alhamis.

Da yake mayar da martani kan lamaɗin, Ajadi, ɗan takarar gwamnan jihar Ogun a inuwar NNPP a zaɓen 2023, ya yaba da mayar da Sanusi II a1 kujerar sarautar Kano.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Ajadi ya yi kira sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bsyero da magoya bayansa su bari a ci gaba da zaman lafiya a jihar.

A cewar tsohon ɗan takarar gwamnan, ya zama wajibi mutane su riƙa mutunta doka da oda a kowane lokaci.

Ambasada Ajadi ya ce:

"Na yi matuƙar farin ciki da dawowar Muhammadu Sanusi II kan karagar sarauta, ina da yaƙinin duba da ilimi da gogewarsa, birnkn Kano zai ƙara samun ci gaba a ƙarƙashinsa.
“Ina jinjina masa bisa mutunta doka ta hanyar lumana da biyayya dokar da tsohuwar majalisar dokokin jihar ta kafa wadda ta kai ga tsige shi.
"Ina masa fatan Allah ya kara masa lafiya tare da fatan bayar da gudunmawar da za ta kawo ci gaban jihar Kano da kasa baki daya inda ya taba rike mukamin Gwamnan Babban Bankin Najeriya."

Kotu ta umarci a fitar da Sanusi

A wani rahoton kuma babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta ba umarnin fitar da Muhammadu Sanusi II daga fadar Sarkin Kano da ke Gidan Rumfa.

Kotun ta kuma hana waɗanda ake ƙara daga gayyata, kamu ko muzgunawa Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero.

Asali: Legit.ng

People are also reading