Home Back

Goron Juma’a

leadership.ng 2024/6/26
Goron Juma’a

Jama’a barkan mu da Juma’a, barkan mu da kasancewa tare da wannan shafi na Goron Juma’a. Shafinda ke ba wa kowa damar mika sakon gaishe-gashensa zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki na kusa, da na nesa.

A yau ma ina dauke da wasu sakonnin gashe-gashen, sai dai kuma kafin na je ga sakonnin masukaratu da suka aiko, sai na fara da mika tawa gaisuwar zuwa ga dukkannin ma’aikatan wannan gidan jarida mai albarka ta LEADERSHIP HAUSA, musamman ma Editana Abdulrazak Yahuza Jere, da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya, kuma da fatan an yi kwalliyar Juma’a tare da kai ziyara lafiya.

Daga Safiyya Idris Aliyu Daudawa

Assalamu alaikum!

Ina gai da dukkan kawayena wadanda muke makarantar Boko da ta Islamiyya tare, da mahaifiyata da mahaifina, sai‘yan’uwana da suka hada da Sulaiman, Muhammadu, da Fatima,da Aisha, da Habibu da aka fisani da Khalifa da ‘yarautarmu Nana Hauwa’u,da fatan an yi Sallar Jumma’a lafiya Allah ya maimaita mana.sako daga Aisha Muhammad:

Assalaikum alaikum!

Al’umar Musulmi baki daya, ina yi wa kowa fatan alkhairi tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Ina gaida iyaye na. mamana da babana ina yi musu fatan alkhairi tare da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, Allah ya maimaita mana. Sannan kuma ina gai da ‘yan uwana yayyena da kannena da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya. Ina gaida kannen mamana da kannen babana tare da yi musu fatan an yi Sallar Juma’a lafiya. Sannan ina gai da ‘yanuwa da abokan arziki da fatan kowa yana cikin koshin lafiya tare da barka da Juma’a. Sako daga Amina Sa’idu

Assalamu alaikum!

Ina yi wa ma’aikatan LEADERSHIP Hausa barka da Juma’a tare da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, ina mika sakon gaisuwa ta ga daukacin Musulmi baki daya tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya. Ina mika sakon gaisuwa ta ga iyayena da ‘yan uwana da abokan arziki tare da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Sako daga Khadija Lawan Sambo

Ina mika sakon gaisuwa ta ga mijina tare da yi masa fatan an yi Sallar Juma’a lafiya, ina mika sakon gaisuwa ta ga iyayena, ina yi musu fatan alkhairi tare da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, ina mika sakon gaisuwa ta ga ‘yanuwa na yayyena maza da mata kannena maza da mata tare da fatan sunyi Sallar Juma’a lafiya. Allah ya sa mu ga ta wani satin amin.

People are also reading