Home Back

El-Rufai vs Uba Sani: Masu Zanga Zanga Sun Dira Gidan Gwamnatin Kaduna

legit.ng 2024/7/4

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - An gudanar da zanga-zanga a gidan gwamnatin jihar Kaduna domin neman a cafke Malam Nasir Ahmad El-Rufai.

Masu zanga-zangar ƙarkashin ƙungiyar Kaduna Citizens Watch for Good Governance (KCWGG) sun mamaye gidan gwamnati da ke Kaduna, domin neman a binciki tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai tare da kama shi.

An yi zanga-zangar neman cafke El-Rufai a Kaduna
Masu zanga-zangar na son Gwamna Uba Sani ya binciki El-Rufai Hoto: @ubasanius, @elrufai Asali: Twitter

Sun buƙaci Gwamna Uba Sani da ya gayyaci jami’an EFCC domin su kama El-Rufai tare da gurfanar da shi a gaban kuliya bisa zargin gwamnatinsa da karkatar da Naira biliyan 423, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Masu zanga-zangar sun riƙa rera waƙoƙi tare da ɗaga alluna da kwalaye masu ɗauke da rubuce-rubuce daban-daban.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙungiyar masu zanga-zangar, Kwamared Victor Duniya ya zanta da manema labarai bayan sun isa gidan gwamnatin jihar Kaduna.

"Mun gode da zuwanku wajen nan yayin da muke nuna fushinmu. Jiharmu ta fuskanci rashin iya sarrafa kuɗaɗe, rashin iya mulki da ɗumbin bashi cikin shekara takwas da suka wuce."
"Babban abin takaici shi ne yadda aka gano an karkatar da N10.5bn na aikin ma'aikatar sarrafa madara a Damau a ƙaramar hukumar Kubau zuwa gina babban kantin Galazy Mall a Kaduna."
"Hakazalika rahoton ya kuma bankaɗo yadda aka riƙa cikawa ƴan kwangiloli kuɗade, biyan kuɗaɗe ga kamfanoni marasa rajista da biyan kuɗaɗen ayyukan da ba a kammala ba waɗanda sun kai sama da N36.5bn"

- Kwamared Victor Duniya

Asali: Legit.ng

People are also reading