Home Back

Shagulgulan Da Aka Yi A Bikin Ranar Dimokuradiyyar Nijeriya

leadership.ng 2024/7/7
Shagulgulan Da Aka Yi A Bikin Ranar Dimokuradiyyar Nijeriya

A ranar Laraba ne Nijeriya ta gudanar da bikin cika shekaru 25 da komawar mulkin farar hula tare da fareti da shagulgula a Abuja babban birnin kasar.

Shugaban kasa Bola Tinubu ya jagoranci manyan baki da dimbin jama’a da suka taru a dandalin Eagles Skuare domin murnar zagayowar ranar dimokuradiyya ta 2024.

Shugaban kasa Tinubu ya duba faretin rundunan sojin Nijeriya da suka kunshi so-jojin kasa da na ruwa da na sama da rundunar ‘yansanda bayan ya isa da misalin karfe 10:00 na safe.

A safiyar ranar ne shugaban kasar ya yi jawabi ga ‘yan Nijeriya domin murnar zagayowar ranar dimokuradiyya.

Ranar 12 ga watan Yuni ce ranar tunawa da dimokuradiyyar Nijeriya wanda ya kawo karshen mulkin soja a shekarar 1999.

Duk da cewa gwamnatin tarayya ta bayar da hutu, mutane da yawa sun fito sa-nye da kaya kala-kala don kallon faretin da bukukuwan wannan rana.

Tinubu tare da rakiyar uwargidansa, Oluremi, ya samu tarba daga mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da sauran jami’an gwamnati.

Bayan rera taken kasa, an tuka Shugaban Tinubu a wata wanda aka zagaya da shi dandalin ‘Eagle Skuare’ tare da daga wa jama’a hannu.

Daga cikin manyan baki da suka halarci taron akwai shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ministoci da mambobin jami’an diplomasiyya da sauransu.

People are also reading