Back to the last page

Ronaldo na harin Chelsea, Real Madrid na son Mbappe

bbc.com 13 minutes ago

Asalin hoton, EPA

Chelsea za ta biya yuro miliyan 70 domin sayen dan wasan Faransa Christopher Nkunku, daga RB Leipzig a watan Yuli a kwantiragin da zai kai har 2028. 

Har yanzu Real Madrid na sha’awar sayen Kylian Mbappe, daga Paris St-Germain, amma sai an cimma wasu sharuda.

Cristiano Ronaldo, na matukar jin sha’awar tafiya Chelsea bayan barinsa Manchester United. 

Matashin dan wasan gaba na kungiyar Lille Jonathan David, dan Kanada, mai shekara 22 ya ce burinsa a yanzu shi ne ya taka leda a gasar Premier.

Bayer Leverkusen na tuntubar kungiyar Club Pachuca domin sayen Luis Chavez bayan ganin yadda dan wasan tsakiyar ya taka rawar-gani a gasar Kofin Duniya a tawagar Mexico.

Dan wasan Real Madrid Eden Hazard na shawarar ritaya daga buga wa kasarsa kwallo a shekara 31, bayan fitar da Belgium din daga gasar Kofin Duniya da wuri.

Kociyan Netherlands Louis van Gaal, mai shekara 71, ya nuna alamun karbar aikin horada da Belgium, kasancewar Roberto Martinez ya kammala wa’adinsa na shekara shida.

Jurgen Klopp ba shi da sha’awar maye gurbin Hansi Flick, idan aka salami kociyan na Jamus, bayan da ya kasa kai tawagar kasar zagayen ‘yan 16 a gasar Kofin Duniya, kasance kociyan na Liverpool ya kuduri aniyar kaiwa har karshen kwantiraginsa a Anfield a 2026.

Darektan bincike na Liverpool Ian Graham, ya kasance jami’in kungiyar na baya-bayan nan da zai bar ta, kuma Anfield na fargabar zai koma Manchester United ne. 

Watakila masu kungiyar Liverpool Fenway Sports Group, su sayar da wani kaso na hannun jarin kungiyar yayin da tattaunawar sayenta a kan fam biliyan 4 ke karuwa.

Back to the last page