Home Back

Ghana: Kishin, na saka rayuwar iyali cikin hadari

dw.com 2024/5/17
Hoto: Gregory Bull/AP/picture alliance

 Zeinab Mohammad Ali,uwar yaya biyu ta fada wa kotu cewa ta aikata laifin ne a yunkurin kare kanta. Sai dai kuma bayanan ba su gamsar da alkalin kotun ba, wanda ya zartas da hukuncin. Irin wannan al'amari daya ne daga cikin misalai a Ghana inda bayan samun tashin hankali sautari saboda kishi mata kan dauki mataki a kan mazajensu ta hanyar   jikkatasu.

Kishi dalilin samun yawan rikici a tsakanin ma'aurata a Ghana

Yanzu haka dai mijin wannan mata yana kwance a asibiti yana yin jinya babbar ayyar  tambaya ita ce ko wanne dalili ne ke janyo kiyayya tsakanin ma'aurata a Ghana. Malama Mannara Abdulmumuni, mai ba da shawarwarin aure a gidauniyar nan ta Peace da’awa ta ce yawanci kishi ne na matan kan yawan janyo tashin hankalin da zaran miji ya bayyana aniyarsa na yin   karin aure.

People are also reading