Home Back

Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Equatorial Guinea

leadership.ng 2024/6/29
Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Equatorial Guinea

Da maraicen yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tattauna da takwaransa na Jamhuriyar Equatorial Guinea, Teodoro Obiang Nguema Mbasogo wanda ke ziyara a kasar, a babban dakin taron al’umma dake birnin Beijing. Shugabannin biyu sun sanar da daga matsayin huldar kasashensu zuwa huldar abota ta hadin-gwiwa bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkan fannoni.

Shugaba Xi ya ce, Sin da Equatorial Guinea, aminan juna ne na arziki. Tun bayan kulla huldar jakadanci a tsakaninsu fiye da rabin karnin da ya gabata, ya zuwa yanzu, har kullum kasashen biyu na goyon bayan juna kan muhimman batutuwan da suka shafi babbar moriyarsu, tare da kulla zumunta mai karfi a tsakaninsu. Xi ya kuma jaddada cewa, karfafa hadin-gwiwa da kasashen Afirka, babban tushe ne na manufofin diflomasiyyar kasar Sin. Kaza lika, Sin na fatan yin kokari tare da kasashen Afirka wajen gudanar da sabon taron kolin dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka wato FOCAC, da kara yayata dadadden zumuncinsu, da fadada hadin-gwiwa, da ci gaba da tattaunawa kan manyan dabarun hadin-gwiwarsu a nan gaba, don bude sabon babi ga raya al’ummomin Sin da Afirka masu kyakkyawar makoma ta bai daya.

Bayan shawarwarin, shugabannin biyu sun kuma halarci bikin rattaba hannu kan wasu takardun hadin-gwiwa a tsakaninsu.

Kaza lika, kafin shawarwarin, shugaba Xi da uwargidansa madam Peng Liyuan sun shirya wani biki a filin dake wajen babban dakin taron al’ummar, don maraba da zuwan shugaba Obiang gami da uwargidansa.

Haka kuma a daren ranar yau, shugaba Xi da madam Peng Liyuan sun shirya liyafar maraba da zuwan shugaba Obiang da uwargidansa a babban dakin taron al’umma dake Beijing. (Murtala Zhang)

People are also reading