Home Back

Sanatoci Sun Tayar Da Jijiyar Wuya Kan Tsarin Kujerun Zama A Majalisa

leadership.ng 2024/5/19
gaza

Biyo bayan shafe hutun kwanaki 40, domin gudanar da hutun bukukuwan Easter da na karamar Sallah, ‘yan majalisar dattawan sun dawo domin ci gaba da zaman majalisa.

Sai dai, zaman farko da suka yi bayan karewar hutun, hatsaniya da cacar baki na kimanin mintuna 30 mai tsanani ta barke a tsakanin sanatocin a babban zauren majalisar sakamakon sauyin wurin zama da aka yi wa kwaskwarima.

Lamarin ya faro ne a yayin da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya fara zayyano sunayen daga cikin sanatocin da suka yi bikin zagayowar ranar hai-huwarsu wadda ta zo daidai lokacin da sanatocin ke a cikin gudanar da hutun na kwana arba’ain.

Haka zalika, cacar bakin ta yi kamari ne bayan da Sanata Sahabi Alhaji Ya’u, na APC daga Zamfara ya tashi daga kan kujerarsa da aka ware masa a cikin fishi, ya kai korafi wurin jagoran majalisar, Sanata Micheal Opeyemi Bamidele na APC daga Ekiti.

Shi ma Sanata Danjuma Goje na APC daga Gombe ta tsakiya, ya bayyana nasa rashin jin dadin ga Opeyemi Bamidele a kan wajen zaman da ake ware masa a zauren majalisar.

Wannan zaman dai, ya kasance zama na farko da sanatocin ke yin amfani da zau-ran majalisar da aka yi wa gyara bayan an shafe wata 19 da rufe babban zauren majalisar.

Bisa tsarin dokokin zaurin majalisar dattawa, sanatocin na zama ne daidai da matsayin kowanne sanata.
Sai dai, kura ta lafa a zauren majalisar bayan da Akpabio ya bukaci jagoran majalisar, Sanata Goje da kuma Sanata Sahabi da su koma su zauna kan Kujerensu, wanda kuma suka bi umarninsa. Hakan kuma ya bai wa Akpabio damar karanta jawabinsa na maraba ga sanatocin, inda daga bisa jagoran majalisar ya kira taron gaggawa don a kawo karshen tayar da jijiyar wuya a kan batun tsarin wajen zaman sanatocin a zauren majalisa.

People are also reading