Home Back

Kotu Ta Dawo da Basaraken da El Rufai Ya Tuge, Ta Ci Tarar Gwamnatin Kaduna N10m

legit.ng 2024/7/3
  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya tube basarake a jihar ana saura kwanaki bakwai ya bar kujerar gwamna
  • El-Rufai ya tube Cif Jonathan Pharaguwa daga sarautar Piriga kan zargin sakaci bayan wani rikici ya barke a jihar
  • Tubabben basaraken ya shigar da kara kotu inda ta yi fatali da korarsa tare da cin tarar gwannatin Kaduna N10m

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Kotun masana'antu ta rusa dakatarwar da Nasir El-Rufai ya yi ga wani basarake lokacin mulkinsa a jihar Kaduna.

Kotun ta dauki matakin ne bayan korafin Cif Jonathan Pharaguwa Zamuna da ke sarautar yankin Piriga a karamar hukumar Lere.

Kotu ta yi fatali da korar basarake da El-Rufai ya yi a Kaduna
Kotu ta ci tarar gwamnatin Kaduna N10m bayan tube basarake da Nasir El-Rufai ya yi. Hoto: Nasir El-Rufai, Industrial Court. Asali: Facebook

Kaduna: Yaushe El-Rufai ya tube basaraken?

Tsohon gwamnan ya dakatar da basaraken ne a ranar 22 ga wata Mayun 2023 kwanaki kadan kafin mika mulki ga Gwamna Uba Sani, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

El-Rufai ya zargi basaraken da sakaci bayan wani rikici a yankin da ya yi sanadin rasa rayuwakan mutane biyu a jihar.

Yayin shari'ar, kotun ta bukaci gwamnatin jihar ta biya basaraken N10m cikin kwanaki 30 saboda asarar da suka jawo masa.

Karin bayani na tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading