Home Back

Kungiyar Yarbawa Ta Caccaki Salon Mulkin Tinubu, Ta Kawo Masa Mafita

legit.ng 2024/6/29
  • Ƙungiyar Yarbawa ta Afenifere ta yi magana kan shekara ɗaya da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya kwashe yana mulkin Najeriya
  • Ƙungiyar ta caccaki manufofin shugaban ƙasan kan tattalin arziƙin inda ta ce ya jefa ƴan Najeriya cikin halin talauci da tsadar rayuwa
  • Afenifere ta buƙaci Shugaba Tinubu ya janye shirin gwamnatinsa na janye tallafin man fetur da yawan jibga haraji da yake yi kan ƴan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar Yarbawa ta Afenifere ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake duba manufofinsa kan tattalin arziƙin ƙasar nan.

Ƙungiyar ta yi nuni da cewa manufofin shugaban ƙasar nan kan tattalin arziƙi sun jefa ƴan Najeriya cikin talauci.

Afenifere ta caccaki manufofin gwamnatin Tinubu
Kungiyar Afenifere ta ce Tinubu ya jefa 'yan Najeriya cikin talauci Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren ƙungiyar, Justice Faloye ya fitar, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Afenifere ta caccaki manufofin Tinubu

Ƙungiyar Afenifere ta caccaki manufofin Shugaba Tinubu kan tattalin arziƙi inda ta yi nuni da cewa abubuwa sun ƙara taɓarɓarewa fiye da lokacin gwamnatin da ta gabace shi, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Ƙungiyar ta bayyana cewa a cikin shekara ɗaya ta gwamnatin Tinubu, tattalin arziƙin ƙasar nan ya shiga halin ƙaƙaniƙayi fiye da lokacin gwamnatin baya.

Ƙungiyar ta kuma caccaki cire tallafin man fetur da mayar da farashin sauya kuɗi na bai ɗaya, inda ta ce waɗannan matakan sun taimaka wajen taɓarɓarewar tattalin arziƙi da jefa ƴan Najeriya cikin wuya.

Wace mafita ƙungiyar ta kawo?

Ƙungiyar ta yi kira ga gwamnati da ta fahimci tattalin arziƙin ƙasar nan ta yadda za ta rage hauhawar farashin kayayyaki, rashin aikin yi, rashin matsuguni da talaucin da ake fama da shi.

Ta buƙaci gwamnati da ta janye shirinta na cire tallafin man fetur da yawan jibga haraji kan ƴan Najeriya.

Ta yi nuni da cewa waɗannan manufofin sun taimaka wajen taɓarɓarewar tattalin arziƙi wanda hakan ya jawo hauhawar farashin kayayyaki da raguwar kuɗaɗen shiga da mutane ke samu.

Tinubu ya rattaɓa hannu kan sabon ƙudiri

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu a kan kudirin dokar taken Najeriya da majalisar dokokin tarayya ta zartar.

Rattaɓa hannun da shugaban ƙasan ya yi kan sabon ƙudirin ya sanya za a dawo da yin amfani da tsohon taken Najeriya na “Najeriya, mun jinjina miki”.

Asali: Legit.ng

People are also reading