Home Back

AKWAI SAURAN ƘURA: Masana sun ce nan da shekara ɗaya Naira za ta yi daraja, ta koma N1200 a Dala 1

premiumtimesng.com 2024/4/29
MAI LAYA KIYAYI MAI ZAMANI: Dala ta yi wa naira duka da gora mai kaca, kwana ɗaya bayan rataya mata laƙanin ki-bugu

Katafaren Bankin Zuba Jari na Duniya, wato Goldmans Sachs, ya yi wa Najeriya kyakkyawan fatan cewa nan da watanni 12 masu zuwa, ya na sa ran darajar Naira za ta ɗaga sama zuwa Naira 1,200 a kowace Dalar Amurka 1.

Ya ce sabbin tsare-tsaren tattalin arzikin ƙasa na kurkusa da Najeriya ta bijiro da su ne za su bayar da wannan sa’idar ɗagawar darajar Naira ɗin.

A cikin wani bayanin da bankin ya yi a birnin New York na Amurka a ranar Alhamis, Goldman Sachs wanda a birnin na New York ne Hedikwatar sa ta ke, ya jinjina wa tunanin da Bankin CBN na Najeriya ya yi kwanan nan, inda ya ƙara danƙara wa masu ramcen kuɗaɗe kuɗin ruwa a Najeriya.

Haka kuma ya ce Naira tiriliyan 1.6 da CBN ya kaɗa wa ƙararrawa, abu ne zai zai iya ‘fidda kitse daga cikin wuta.’

Naira dai ta rasa kashi 70 bisa 100 na darajar ta a cikin watanni 9 zuwa yau, inda ta tashi daga N750 duk Dala 1, har ta kai N1,680 duk Dala 1.

A yanzu dai Dala ta na Naira 1,500 da ɗoriya, a daidai lokacin da raɗaɗin tsadar rayuwa ke ci gaba da kwankwatsar talakawa da masu hali, inda farashin abinci, kayan masarufi da sauran kayayyakin amfani duk sun tashi, tun bayan tashin Dala da cire tallafin fetur.

 
People are also reading