Home Back

Hukuma A Kano Ta Damƙe Mutane 2 Kan Zargin Zamba

leadership.ng 2024/11/4
Hukuma A Kano Ta Damƙe Mutane 2 Kan Zargin Zamba

Hukumar karɓar korafe-korafen jama’a da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ta damƙe wasu mutane biyu tare da gayyatar wasu sakatarori guda uku, domin amsa tambayoyi kan badaƙalar sayar da fam ɗin aiki a ofishin shugaban ma’aikata.

Shugaban hukumar Muhuyi Rimin-Gado, ne ya bayyana hakan a Kano, inda ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin ganowa da gurfanar da waɗanda ke da hannu a badaƙalar zambar da ta shafi dubban masu neman aiki.

Muhyi ya ci gaba da cewa, a binciken farko da aka gudanar an gano wasu ayyukan damfara a ofishin shugaban ma’aikata da hukumar kula da makarantun sakandire ta jihar Kano da ta kula da ma’aikatan lafiya.

Ya ce mutanen biyu da ake tsare da su suna bayar da haɗin kai wajen gudanar da binciken lamarin da ya kai ga rufe wata kafar ɗaukar ma’aikata ta bogi, inda ya ce hukumar na ƙoƙarin kawar da cin hanci da rashawa da kuma tabbatar da an yi adalci a badaƙalar ayyukan yi da ake damfarar dubban masu neman aikin.

A cewarsa, binciken da ake yi zai fallasa tare da gurfanar da waɗanda suke damfara wajen sayar da fam ɗin aikin, kamar yadda gwamnatin jihar ta ba da umarnin yin bincike sosai kan lamarin tare da gurfanar da waɗanda aka samu da hannu a gaban kuliya.