Home Back

Huldar Abotar Dindindin Tsakanin Sin Da Kazakhstan Na Samun Ci Gaba Zuwa Sabon Mataki

leadership.ng 2 days ago
Huldar Abotar Dindindin Tsakanin Sin Da Kazakhstan Na Samun Ci Gaba Zuwa Sabon Mataki

Sin ta mai da Kazakhstan a matsayin abokiyarta ta hulda ta dindindin bisa manyan tsare-tsare a dukkanin fannoni. Wannan matsayi mai muhimmanci ya zama abin misali ga sauran kasashe makwabta wajen hadin kai da samun moriya tare tsakanin kasa da kasa. To yaya za a ciyar da wannan hulda gaba a daidai wannan muhimmin lokaci na samun bunkasuwa da farfadowar al’umommin kasashen biyu? Ziyarar aikin da shugaban kasar Sin Xi Jinping yake yi a kasar Kazakhstan daga ran 2 zuwa ran 4 ga wata ya ba da amsa. A yayin ziyararsa, shugabannin kasashen biyu sun yi shawarwari masu armashi, da kulla yarjejeniyar hadin gwiwa, inda suka bayyana fatansu na ingiza kafa wata kyakkyawar makoma ta bai daya ta zumunci mai dorewa da amincewa da juna da cin moriya da magance matsaloli da kuma more wadata tare.

Shugabannin biyu sun halarci bikin kaddamar da hanyar sufurin kaya mai saurin tafiya da ta hada Sin da Turai wadda ta ratsa tekun Caspian, ta kafar bidiyo. A karon farko, motocin kasar Sin sun yi jigilar kayayyaki zuwa tashar jirgin ruwa ta tekun Caspian kai tsaye ta hanyoyin mota, lamarin da ya alamta kafuwar tsarin mu’ammala da cudanya da juna ta mabambantan hanyoyi. Ban da wannan kuma, burin da aka sa gaba na karawa juna kwarin gwiwa, wato samun ninkin yawan kudin cinikinsu. Wadannan tsare-tsare sun dace da halin da ake ciki yanzu da makomar nan gaba, kuma ya kasance kyakkyawar hange nesa wajen samun bunkasuwa da hanzarta kai ga sabon matsayin hadin gwiwarsu, da ma inganta huldarsu ta zamanintar da al’umomminsu. (Amina Xu)

People are also reading