Home Back

JUNE 12: Jawabin Tinubu Zancen Danmagori Ne da Kashe Guiwar Ƴan Kasa Wajen Makomar Najeriya, Ahmed Ilallah

premiumtimesng.com 2024/7/5
RANAR DIMOKARAƊIYA: Mu tashi tsaye mu hana idanuwanmu bacci har sai mun shaida cikar burin mu na cigaban Najeriya – Tinubu

Anya kuwa alamu basu soma bayyann ba, shima wannan mulkin na Tinubu kamar na Buhari ne, koma zai gazawa na Buharin ma. Kai kalamun mutum fa kan bayyana karfin zuciyar sa.

Duk da cewar Yan Nijerya sun kagu da suji mai Shugaba Tinubu zai ce, a lokacin da ya cika shekara guda a kan karagar mulki, a lokacin da dimokaradiyya na shekara 25 ba tare da tangarda ba.

Wannan kaguwa ta sauraron Tinubu sai da ta kawo sa’insa tsakanin manyan masu hidimta masa Bayo Onanuga da Ajuri Nglale a kan ko zaiyi jawabi ranar 29 ga watan Mayu a gaban hadakar Yan Majalissar Kasa ko aa.

Mu de a Arewacin Nijeriya zamu iya cewa demokaradiyyar kamar annoba ta zame mana.

Abin kamar wasa tarihin zaman lafiya Arewa ya chanja, bala’in tashin hankali, ta’addanci da rashin tsaro ya mamaye Arewan.

Talauchi da koma baya ya aure mu, muna neman zama tamkar bayin wasu a wannan kasa.

Ita kanta shekarar dayan Tinubu tafi zama mafi kalubale, tsanani da rashin tabbas ga Yan Nijeriya.

Yan Nijeriya sun maida hankali don suji hikima da tsare tsaren Shugaba Tinubu a kan makomar Nijeriya a nan gaba. Da nuna kwarewar sa wajen fidda kasar nan a halin da take ciki sabanin shugabannin baya.

Amma sai gashi a ranar dimokaradiyyar da Tsohon Shugaba Buhari ya mayar ranar 12 ga watan June din da ake ga matsin lambar su Tinubun ne ya sanya shi yin hakan, sai gashi jawabin nasa babu wani abu na karfin gwiwar ga Yan Kasar na imani ga dimokaradiyyar.

Abin takaicin sai gashi Shugaba Tinubun a jawabin nasa ya bige da zancen Dan Magori wasa kanka da kanka.

Babu komai a ciki sai yabon Yan NADECO da yan June 12, su Abiola, Kudirat, Falana da shi kansa da wasu tsirarun anokan birmin su daga Arewa da kuma jaridun yankunan su.

Karin takaicin shine babu wani batu a kan halin tsaron da kasa take ciki, duk da cewa a wannan makon ne a ka kai mummunan hari jahar katsina, yayin da mutane dewa suka rasa rayukan su.

Shekara wannan ta Tinubu tana data cikin shekarun da a ka fi hallaka Yan Nijeriya, musamman mutanen Arewa, jirgin sojoji ma ya kashe muatne haka sidan a kauyen Kurmin Biri a jahar Kaduna, wai ance kuskure ne.

Amma fa tun daga farko har aya babu wani batu na kwarin gwiwa a kan makomar tattalin arziki, tsaro da walwalar Yan Nijeriya a dalilin demokaradiyya

Wannan ya sake tabbatarwa Yan Nijeriya lalle akwai sauran rina a kaba, wajen dacen shugabannin da zasu iya taimakon wannan Yan Kasa sa ingantaccen mulki irin na Dimokaradiyya.

People are also reading