Home Back

Sanusi II vs Aminu Ado: An Ba Gwamna Abba Lakanin Warware Rikicin Sarautar Kano

legit.ng 2024/7/3
  • Wata ƙungiya ta caccaki gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf kan rikicin masarautar Kano da ake ta taƙaddama a kai
  • Ƙungiyar ta ce gwamnan ya jawo abin kunya ga jihar ta hanyar kin mutunta doka kan umarnin kotu da ya hana shi rushe sababbin masarautun jihar
  • Ta buƙace shi da ya bayar da haƙuri ga al'ummar jihar Kano da ƴan Najeriya baki ɗaya tare da mutunta hukuncin da kotu ta yanke

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Ƙungiyar 'Concerned Citizens of Kano' ta buƙaci Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya gaggauta ba da haƙuri kan abin da ya yi wanda ya janyo rikicin Masarautar Kano.

Ƙungiyar ta ce gwamnan ba wai kawai bai mutunta al’adun gargajiyar jihar Kano kaɗai ba, har ma ya nuna rashin mutunta ɓangaren shari’a da bin doka da oda.

Kungiya ta caccaki Gwamna Abba Kabir Yusuf
An bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba al'ummar Kano hakuri Hoto: Abba Kabir Yusuf Asali: Facebook

Ƙungiya ta caccaki Gwamna Abba

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Kwamared Mustapha Aliyu ya rattaɓawa hannu, cewar rahoton jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyar ta ce ta hanyar sauya fasalin masarautar Kano, Gwamna Abba ya cutar da al’ummar Kano, ya zubar da martabar al’adun jihar, rahoton jaridar Independent ya tabbatar.

Ta yi nuni da cewa gwamnan bai mutunta doka ba ta hanyar sake naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano da rushe sababbin masarautun jihar.

A cewar Mustapha Aliyu, abin da ya yi ya haifar da rashin jituwa, ya haifar da rarrabuwar kawuna, da kuma barazana ga zaman lafiyar jihar da ma al’ummar ƙasar baki ɗaya, domin haka dole ne ya nemi afuwar ƴan Najeriya. 

Wace shawara aka ba Gwamna Abba?

Ƙungiyar ta buƙaci Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya gaggauta ɗaukar matakin shawo kan wannan rikici ta hanyar bayar da haƙuri ga al’ummar jihar Kano da ma ƴan Najeriya baki ɗaya kan abin da ya yi wanda ya jawo abin kunya ga jihar.

"Dole ne kuma ya mutunta hukuncin da kotu ta yanke kuma ya bar tsarin shari'a ya gudanar da aikinsa."
"Ya ɗauki matakai domin warware rikicin cikin gaskiya, adalci, da mutunta haƙƙi da mutuncin duk ɓangarorin da abin ya shafa.
"Dole ne ya tabbatar da kare rayuka da dukiyoyi, tare da inganta zaman lafiya a tsakanin ɗaukacin al'ummar jihar Kano."

- Kwamared Mustapha Aliyu

Hakimai sun shiga ruɗani a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa yayin da ake ci gaba da dambarwar sarautar masarautar Kano, wasu hakimai da masu saurautar gargajiya sun shiga ruɗani.

Wasu da dama daga cikin hakimai da masu rike da masarautun gargajiya sun rasa wanda za su yiwa mubaya'a a tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero.

Asali: Legit.ng

People are also reading