Home Back

Spain Ireland da Norway sun caccaki Isra'ila kan Falasdinu

dw.com 2024/7/1
Hoto: Abed Rahim Khatib/dpa/picture alliance

Kasashen Spain da Ireland da kuma Norway za su fitar da sanarwar hadin gwiwa da kakkausar murya kan Isra'ila, bayan martani mai zafi game da amincewarsu da Falasdinu a matsayin 'yantacciyar kasa mai cin gashin kanta a yau.

Ministan harkokin wajen Spain Jose Manuel Albares ya ce sanarwar da kasashen uku za su fitar za ta jaddada aniyarsu ta amincewa da 'yancin Falasdinawan, kuma ita ce matsayarsu a ko yaushe.

Isra'ila dai ta soki ra'ayin kasashen uku cikin wani martani mai zafi.

People are also reading