Home Back

Shugaba Biden na ci gaba da fuskantar barazana a takararsa

bbc.com 2024/10/7
Joe Biden

Asalin hoton, Reuters

Ana ci gaba da kunno wa Shugaba Biden na Amurka wuta daga cikin jam'iyyarsa ta Democrat, kan ya hakura da takarar zaben da za a yi a watan Nuwamba, a maye gurbinsa a takarar, saboda alamun gazawar da ake gani a kansa.

Na baya-bayan nan a wannan kira shi ne wani jigo a majalisar wakilai Adam Smith, wanda ya bi sahun takwarorinsa na jam’iyyar ta Democrat da cewa Biden mai shekara 81, ba shi ya fi dacewa da wannan takara ba.

Ƴan Democrat da ke neman sauya Biden a takarar na hakan ne sakamakon rashin tabuka abin a-zo-a-gani da Mista Biden ya yi a muhawararsa da abokin hamayyarsa na Republic, Donald Trump.

A makon da ya gabata Mista Biden ya mayar da martani ga irin wannan kira na ya ajiye takarar shugabancin kasar a jam’iyyarsu ta Democrat bayan da kiran ya ci gaba da ruruwa da karin muryar wani kusa a jam’iyyar- dan majalisar wakilai Lloyd Doggett.

Dan majalisar ya kasance na farko da ya fito baro-baro ya nemi shugaban da ya hakura da takarar, kasancewar sauran masu maganar na yi ne a bayan fage.

A lokacin Shugaban ya ta’allaƙa abin da ya sa ake neman da ya yi hakan da yadda ya tunkari muhawararsa ta farko da Donald Trump, ya danganta matsalar rashin kataɓus din da yawan tafiye-tafiye, amma ba shekaru ko rashin kaifin basirarsa ba.

A wannan karon Mista Biden, wanda zai karbi bakuncin taron koli na kungiyar tsaro ta NATO, bai saurara wa masu ganin wallen nasa ba.

Ya ce yana nan daram a wannan takara, ba ma takarar kadai ba, ya ce zai ma doke Donald Trump ne a zaben.

Ya yi wannan bugun kirji ne a cikin wata wasika da ya aika wa ’yan majalisar dokokin Amurka na jam’iyyarsa ta Democrat, kasancewar yana ganin yayin da ‘yan majalisar ke komawa Washington kila kiran ajiye takarar tasa ya kara amo, a don haka ya yi wannan kan-da-garki.

Mista Biden bai ma tsaya a nan ba, ya ma kalubalanci duk wanda yake ganin zai iya da cewa ya fito su kara a babban taron jam’iyyar.

Shi ma wani tsohon jakadan Amurka a kungiyar tsaron ta NATO a hirarsa da BBC ya ce ba ya ganin Mista Biden zai iya cin zaben na wannan shekara ta 2024.

Kurt Volker, ya ce yana ganin abin da ya fi dacewa shi ne jam’iyyar ta samu wani dantakara kawai amma ba Biden ba.

Ya ce: “ Ina ganin idan muna son yanayi na yadda za ka kasance kana da jagora, da ya danfaru ga NATO, kuma mutumin da ke da kudurin nasarar Ukraine a kan ainahin hadarin barazanar Rasha, ina ganin zai fi kyau ga ‘yan Democrat su sami wani dan takara da za su musanya.’’

Ba wani da ya fito fili cikin masu kalubalantar Biden , zuwa yanzu, illa dai yawancin masu ganin ba zai iya fitar wa jam’iyyar tasu kitse a wuta ba a zaben na watan Nuwamba na tattaruwa ne a karkashin inuwar masu ra’ayin cewa mataimakiyar shugaban kasar Kamala Harris, ita ya kamata ta karbi tutar takarar.

Ita ma dai wasu na ganin anya kuwa idan har aka ba ta takarar za ta iya karawa har ta kayar da Trump?

A wata hira da aka yi da shi ranar Juma’a Mista Biden ya ce Ubangiji ne kawai zai iya shawo kansa, ya ajiye wannan takara ta zaben shugaban kasa.

Abin da kuma ba a kai ga hakan ba zuwa yanzu.

Illa dai masu shakkun kan iya takarar tasa bisa yawan shekaru da raunin kwakwalwarsa da suke gani a yanzu na ci gaba da karuwa da fitowa fili, shi kuwa yana ci gaba da tsayuwar gwaman jaki, da cewa ba inda zan je.

A wani zazzafan taron manema labarai, mai magana da yawon shugaban Amurkar, Karine Jean-Pierre, ta yi watsi da abin da wasu ke zargi cewa Biden na fama da wani rashin lafiya da ba a bayyana ba.

People are also reading