Home Back

Tsarin Tsaron Duniya Na Sin Da Na Amurka Wane Ne Ya fi Dacewa Da Muradun Duniya?

leadership.ng 2024/7/5
Tsarin Tsaron Duniya Na Sin Da Na Amurka Wane Ne Ya fi Dacewa Da Muradun Duniya?

A ranar Lahadi ne ministan tsaron kasar Sin Dong Jun ya gabatar da tsarin kasar Sin game da harkokin tsaron duniya a yayin rufe taron tattaunawa na Shangri-La karo na 21 a Singapore, kuma ya gabatar da ra’ayoyin kasar Sin game da warware matsalolin tsaron duniya da mahangar duniya, kana, ya jaddada matsayin kasar Sin kan batun Taiwan, da kuma batun tekun kudancin kasar Sin.

A cikin jawabinsa, janar Dong ya bayyana cewa, manufar kasar Sin na gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga bil’adama, tare da shirin raya kasa da kasa, da shirin samar da tsaro na duniya, da shirin wayewar kai a duniya, ya yi daidai da yanayin tarihi da kuma mayar da martani ga burin mutane a duniya don samun ingantacciyar rayuwa.

Idan aka kwatanta da jawabin da sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin ya gabatar a ranar Asabar, jawabin Dong ya mai da hankali kan batutuwan da suka shafi shiyya-shiyya da ma duniya baki daya, tare da yin la’akari da muradun daukacin bil’adama, shi kuma mista Austin na Amurka ya fi mayar da hankali kan Amurka da kawayenta da abokan huldarta a yankin. Jawabinsa ya ta’allaka ne kawai a kan bukatunsu na son kai da muradun kasarsu, kuma ya yi watsi da kasantuwar ASEAN a cikin batutuwan hadin gwiwar yanki.

Jigon jawabin na Austin ya bayyana cewa, Amurka na da burin cimma jagoranci a yankin “Indo-Pacific” ta hanyar tsare-tsare irin su AUKUS, QUAD da sauran kawancen soja, yayin da kuma take wayincewa kan samar da “Indo-Pacific kwatankwacin NATO”. Wanda rashin fahimta ce ta dabara da kuma karkatacciyar fahimtar tsaro da masana suka ce yana haifar da hargitsi da rikici har ma da yaki, maimakon samar da tsaro da kwanciyar hankali.

Bisa la’akari da rikice-rikicen da ke faruwa a Turai da Gabas ta Tsakiya, Asiya Pasifik na daya daga cikin yankuna kadan a duniya da har yanzu ke samun kwanciyar hankali a yau. Masu lura da al’amuran yau da kullun sun ce, a bayyane yake wane tsarin tsaro na duniya, na kasar Sin ko Amurka, ya fi dacewa da muhimman muradu da matsalolin tsaro na galibin kasashen duniya. (Yahaya)

People are also reading