Home Back

Majalisar Dattawa Ka Iya Sauya Tunani Kan Dakatar da Sanata Abdul Ningi

legit.ng 2024/5/19

FCT Abuja - Majalisar dattawa ta bayyana cewa da yiwuwar ta sake duba matakin da ta ɗauka na dakatar da Sanata Abdul Ningi mai wakiltar mazaɓar Bauchi ta Tsakiya.

An dakatar da Ningi na tsawon watanni uku saboda ikirarin da ya yi a wata hira da sashen Hausa na BBC cewa majalisar tarayya ta yi cushe a kasafin kudin 2024.

Majalisar dattawa.
Da yiwuwar sanatoci su sake nazari kan dakatar Sanata Abdul Ningi Hoto: NGRSenate Asali: Twitter

Sanata, wanda Femi Falana SAN ke goyon baya, ya ba shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, mako ɗaya ya soke dakatar da shi ko su fara shari'a.

Da yake mayar da martani, Akpabio ya ce ba da son zuciyarsa ya dakatar da Ningi ba, mataki ne da sanatoci 108 cikin 109 suka amince da shi, Daily Trust ta ruwaito.

Da yake magana yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Litinin, kakakin majalisar dattawa, Yemi Adaramodu, ya ce za a duba batun Ningi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, majalisar dattawa za ta sake duba batun dakatar da Ningi bayan sanatoci sun dawo daga hutu ranar Talata.

Sanata Adaramodu ya jaddada cewa duk wani hukunci na dawi da Ningi zai sbuƙaci kowane mamban majalisar dattawa.

Ya kuma yi bayanin cewa ba Akpabio ya dauki matakin dakatar da Ninhi shi kaɗai ba, sai dai mataki ne da sanatoci 108 suka ɗauka har da Ningi da kansa.

“Sanatoci 109 ban da Sanata Ningi sun yanke shawarar cewa za a yi wa Sanata Ningi hukunci mai sauki na dakatar da shi na tsawon watanni uku daga ayyukan majalisa.

"Saboda haka waɗannan sanatoci 108 da una ɗauki wannam mataki sune za su iya kiran Sanata Nindi ya dawo cikin majalisa.

"Muna hutu kusan makonni hudu kenan. Don haka idan muka koma gobe (Talata), shi abokin aikinmu ne, idan ya ba da haƙuri, to ‘yan majalisar dattawa za su duba, mu yi abin da ya dace."

Asali: Legit.ng

People are also reading