Home Back

Napoli Ta Nada Antonio Conte A Matsayin Sabon Kocinta

leadership.ng 2024/6/29
Napoli Ta Nada Antonio Conte A Matsayin Sabon Kocinta

Kungiyar kwallon kafa ta Napoli ta sanar da nada Antonio Conte a matsayin sabon mai horas da ‘yan wasanta a yau Laraba.

Conte ya kulla yarjejeniya da kungiyar da ke buga gasar Seria A har zuwa karshen watan Yunin 2027.

Shugaban kungiyar Aurelio De Laurentiis, ya nuna jin dadinsa kan daukar Conte.

Ya ce Conte hazikin mai horaswa ne kuma ya aminta da irin tarihin da ya kafa a baya, shi ya sa ya amince wajen daukarsa.

Conte ya taba horas da kungiyoyin Chelsea, Tottenham da Juventus a baya.

A nasa bangaren, Conte ya ce Napoli babbar kungiya ce wadda yake da yakinin za su kafa wani tarihi tare.

People are also reading