Home Back

Shugaban Kenya mayar da dokar haraji ga majalisa

dw.com 6 days ago
Kenya | Jami'an tsaron lokacin zanga-zanga a Kenya
Jami'an tsaron lokacin zanga-zanga a Kenya

Shugaba William Ruto na Kenya ya yi watsi da dokar fadada haraji da majalisar dokoki ta amince da ita, abin da ya haifar da zanga-zanga a kasar, inda ya sake mayar da dokar majalisar domin gyare-gyare. Majalisdar tana zama na musamman karkashin tsauraran matakan tsaro, inda majalisar ta amince da tura sojoji kare gine-gine masu muhimmanci lokacin zanga-zanga.

Tun farko Kungiyar likitoci ta kasar ta tabbatar da mutuwar fiye da mutane 20 kana wasu kimanin 30 suka jikata sakamakon zanga-zangar da aka fuskanta a fadin kasar a wannan Talata da ta gabata, domin kiyayya bisa sabuwar dokar da majalisar dokokin kasar ta amince ta fadada haraji kan kayayyaki a kasar.

Wannan na zuwa lokacin da masu zanga-zangar ke cewa za su sake komawa kan tituna a gobe Alhamis, domin nuna mutuntuwa ga masu zanga-zangar da suka mutu lokacin artabu da jami'an tsaro, kamar yadda masu shirya zanga-zangar suka nunar a shafukan sada zumunta musamman na X ko kuma Twitter. Ana sa bangaren Shugaba Ruto na kasar ta Kenya ya yi zargin cewa masu tayar da zaune tsaye sun karbe ragamar zanga-zangar.

People are also reading