Home Back

Shin abincin kamfani na da illa ga lafiyarku?

bbc.com 2024/5/14
Bowls of factory-made breakfast cereals

An alaƙanta abincin gwangwani ga matsalolin zuciya fiye da 30 da cutar daji da kuma rashin natsuwa.

Sun ƙunshi fiye da kashi 50 cikin 100 na matsakaicin ci-makar Amurka da Birtaniya kuma suna ƙara samun karɓuwa a sassan duniya.

Mene ne abincin gwangwani?

Babu hanya ɗaya ta bayanin abincin gwangwani amma suna ƙunshe da sinadaran girkin da ba a amfani da su a gida.

Akasarinsu sinadarai ne da abubuwan da ke sauya launin abinci da zaƙaƙa abinci da ake amfani da su domin inganta yanayin abinci da ɗanɗano.

Misalai su ne lemon gwangwani da alawa da naman kazar da aka soya sama-sama. Sai dai suna iya shafar abinci kamar burodi da madarar yogot da abincin da ake haɗawa da hatsi.

Yadda abincin gwangwani ya bambanta da wanda aka sarrafa

Don taimaka wa mutane gane nau'ikan abinci, ana yawan amfani da wani tsari na kasa su gida huɗu.

Sune ɗanye da wanda aka ɗan sarrafa da kayan abincin da aka sarrafa da abincin gwangwani da waɗanda aka sauyawa launi.

Chart showing four categories of food ranging from unprocessed/minimally processed to ultra-processed
Bayanan hoto, To request set of 3 graphics: 1. Complete the translations here: https://tinyurl.com/2s3pusss 2. Fill-in the commissioning form https://bit.ly/ws_design_form and this Title in English: Ultra processed foods and health - 2024030702

Abincin da aka sauyawa kala ko ɗanɗano haɗakar abinci ne kamar itatuwa da ganyayyaki da gyaɗa da ƙwai da kayan ɗanɗanon da aka sarrafa.

Misali, burodin da aka yi da alkama da ruwa da gishiri da sinadarin da ke sa abinci ya tashi wato 'yeast', abinci ne da aka sarrafa.

Sai dai, idan aka yi amfani da kayan sauya launi ko abin da ke hana abinci lalacewa, burodin zai zama wanda aka sarrafa.

Ta yaya zan gane abincin da aka sarrafa?

Abincin da ke ɗauke da sinadari fiye da biyar da yiwuwar sarrafaffe ne, in ji ƙwararriya kan lafiyar al'umma, Farfesa Maira Bes-Rastrollo ta jami'ar Navarra da ke Sifaniya.

Ma fi yawan lokuta, abincin da aka sarrafa na da yawan gishiri da sukari da curarren kitse. A Birtaniya da wasu ƙasashen, ana rubuta hakan a jikin gwangwanin.

Yana iya zama abinci ɗanye da bai lalace ba, amma yana iya ɗaukar lokaci kafin ya lalace saboda saka kayan da zai hana shi lalacewa. Duba jikin gwangwanin ko akwai sinadarai kamar sodium benzoate da nitrate da sulphite da BHA da BHT.

Ta yaya abincin kamfani ya yaɗu a sassan duniya?

Mutane a Birtaniya da Amurka su ne suka fi cin abincin da aka sarrafa.

A 2023, abincin kamfani shi ne ya kai kashi 58 cikin 100 na manya matsakaita a Amurka da ke cin sinadaran ƙara kuzari da kashi 66 cikin 100 na yara.

Alƙaluman sun ragu da kashi ɗaya na manyan Birtaniya da yara.

A ƙasashen Asiya kamar Koriya ta Kudu da Japan da kuma ƙasashen da ke Kudancin Amurka kamar Brazil da Chile, abincin gwangwani shi ne ke kai kashi 20 zuwa 30 na sinadaran kuzari na mutane. A Afirka ta Kudu, alƙaluman sun kai kashi 39 cikin 100.

Shin akwai illa a cin abincin kamfani?

Babu wata sahihiyar shaida game da tasirin da cin abincin kamfani ko gwangwani ke yi kan lafiya.

Sai dai wani bincike a baya-bayan nan da aka wallafa a mujallar British Medical - game da bayanai daga mutum miliyan 9.9 a duniya - an alaƙanta shi da:

  • Haɗarin mutuwa daga cututtukan zuciya kamar bugun zuciya da bugun jini
  • Ƙibar da ta wuce ƙima
  • Nau'in ciwon suga na biyu
  • Matsalolin barci
  • Damuwa

Sai dai ba a iya tantance ko abincin da aka sarrafa ne ya haifar da cututtukan ko kuma cewa galibinsu na ƙunshe da kitse mai yawa da sukari da kuma gishiri.

Waɗnnan su ne ke janyo ƙaruwar ƙiba da nau'in ciwon suga mataki na biyu da ciwon zuciya da wasu nau'ikan cutar daji.

Matsananciyar ƙiba

Ƙiba ce tasiri na farko wanda ake iya gani na illar cin abincin gwangwani," in ji Chris van Tulleken, masani kan garkuwar jikin mutum daga jami'ar University College da ke London, wanda kuma ya taɓa yin rubutu kan abinci mai gina jiki.

"Waɗannan abincin dama suna da yawan kitse da gishiri da suga. Sai dai suma an tsara s ne - ta hanyar launinsu da ɗanɗanonsu - da za a iya ci fiye da ƙima."

Wani bincike daga Jami'ar Imperial College ya nuna cewa fiye da al'ummar duniya biliyan ɗaya - mutum ɗaya cikin takwas - suna rayuwa da matsananciyar ƙiba.

Ya ce a tsakanin 1992 da 2022, matsananciyar ƙiba ta ninka a tsakanin mata manya, ta ninka sau uku ga maza manya sannan ta ƙaru sau biyar a tsakanin yara.

Sannan binciken baya-baya daga Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO da ƙungiyar da ke sa ido kan harkokin lafiya ta Global Health Observatory daga 2016, sun ce fiye da kashi 28 cikin 100 na manya a nahiyar Amurka na fama da matsananciyar ƙiba yayin da ake da kashi 26 cikin 100 a Turai sai kashi 19 cikin 100 a yankin gabashin tekun mediteriya da kashi 9 cikin 100 a Afirka.

WHO ta ce mutum biliyan 2.8 na mutuwa duk shekara saboda matsananciyar ƙiba.

"Akasarin ƙasashen duniya, abincin gwangwani a yanzu ya fi arha kuma an fi saurin samun sa, a kan abincin gargajiya da ke kasuwanni," in ji Dakta Claire Johnson, wata ƙwararriya kan abinci mai gina jiki a asusun kula da ƙananan yara, Unicef.

Ciwon sukari

Ƙarin mutane a duniya a yanzu na da nau'in ciwon suga na 2, a cewar ƙungiyar masu fama da ciwon suga.

"Gishiri da suga da kuma kitsen da ke cikin abincin gwangwani duka na da haɗarin haifar da mataki na biyu na ciwon suga - da kuma abinci mai yawan sinadaran ƙara kuzari da ƙarancin abubuwan gina jiki," in ji Jaakko Toumilehto, wani farfesan lafiyar al'umma a jami'ar Helsinki.

Yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka sun fuskanci ƙaruwa a yawan mutanen da ke ɗauke da ciwon suga na biyu.

"Galibin waɗannan ƙasashen ba sa samar da abinci da kansu," in ji Farfesa Toumilenhto. "Abincin gwangwani ya fi sauƙi wajen ajiya da jigila. shi ne abin da kamfanonin sarrafa abinci suka fi aikawa."

Rashin abinci mai gina jiki

Abincin gwangwani yana janyo rashin abinci mai gina jiki a ƙasashe da dama na kudu da hamadar sahara, in jiDakta Johnson.

"Suna da ƙarancin sinadaran gina jiki da ke ƙunshe a abincin gargajiya kamar sinadaran iron da mineral da vitamins," in ji ta.

Sai dai masana kimiyya a jami'ar Purdue da ke Amurka ta ce abincin gwangwani na iya samun alfanu, kamar:

  • Samar da sinadaran gina jiki kamar vitamin E da calcium
  • Samar da zaɓin mafi araha a kan abincin da ba a sauyawa ɗanɗano ba ga mutane da ba su da ƙarfin samu
  • Rage ɓarnar abinci da yiwuwar cin abinci mai gurɓata ciki

Gidauniyar abinci mai gina jiki ta Birtaniya - The British Nutrition Foundation, wadda ke aiki tare da karɓar tallafi daga kamfanonin abinci, ta yi bayani cewa ba duka abincin gwangwani suka zo ɗaya ba.

"Nau'in abinci da suka faɗo ƙarƙashin abincin gwangwani, kamar abincin da aka yi daga hatsi da burodi da madarar yogot mara maiƙo da gishiri da sukari." in ji Sara Stanner, daraktan ɓangaren kimiyya na gidauniyar.

"Duka waɗannan hanyoyin samun muhimman sinadaran gina jiki ne."

Wane mataki aka ɗauka a kan abincin gwangwani?

Gwamnatin Birtaniya ta sanya haraji kan lemon kwalba a 2018 sannan wasu kamfanoni da dama sun rage yawan sukari a wani salo na martani.

A 2023, Colombia ta sa harajin kashi 10 cikin 100 - wanda zai ƙaru a gaba - kan lemon kwalba da abincin gwangwani.

A 2016, Chile - wadda take da yaran da suka fi matsananciyar ƙiba a duniya - tana liƙa takardar gargaɗi kan abincin da ke da yawan sukari da maiƙo da sinadaran ƙara kuzari.

Labels on food packaging in Chile warning of high calorie, fat and sugar content

Asalin hoton, Getty Images

Ta kuma taƙaita tallar abinci mai yawan sukari da gishiri da sinadaran bada kuzari ga yara.

Sai dai cikin shekaru huɗu bayan samar da matakan, an ci gaba da samun ƙaruwar yara masu kibar da ta wuce ƙima.

People are also reading