Home Back

A KANON DAI: Babbar Kotun Kano ta ce a tura wa Ganduje, matar sa da ɗan sa sammaci ko ta shafin su ne na Facebook, ya wadatar

premiumtimesng.com 2024/7/4
A KANON DAI: Babbar Kotun Kano ta ce a tura wa Ganduje, matar sa da ɗan sa sammaci ko ta shafin su ne na Facebook, ya wadatar

Babbar Kotun Kano ta bada umarnin aika wa tsohon Gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje sammaci, “ta hanyar da zai gani, ko da kuwa ta shafin Facebook ne.

Kotun ta ƙara da cewa a aika sammacin ga matar sa Hafsat Ganduje da kumar ɗan sa, Umar Ganduje.

A ranar Laraba xe Babbar Kotun Jihar Kano ta bayar da umarnin na yi wa Shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Ganduje da matar sa ​​Hafsat da wasu mutane biyar.

Gwamnatin Jihar Kano ce dai ta maka Ganduje a matsayin wanda ake ƙara na ɗaya da matar sa, Hafsat a matsayin wacce ake ƙara ta biyu da sauran su zuwa kotu bisa tuhumar su da laifin cin hanci da rashawa da karkatar da kuɗaɗen da suka kai biliyoyin nairori.

Sauran a cikin sauran waɗanda aka maka su kotun, sun hada da Abubakar Bawuro wanda ake ƙara na uku. Umar Ganduje, wanda ake kara na huɗu, Jibrilla Muhammad da na biyar shi ne Kamfanin Safari Textiles Ltd da Lesage General Enterprises a matsayin na 7 da 8.

Kotun ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Amina Adamu, ta bayar da wannan umarni ne biyo bayan buƙatar da lauyan Gwamnatin Jihar Kano, Zahradeen Kofar-Mata ya yi, wanda ke kare lauyan mai shigar da ƙara, Ya’u Adamu.

Baya ga wannan tuhuma da ake yi wa Ganduje a Kano, a Abuja ma wasu masu ruwa da tsakin APC sun maka shi kotu, su na neman a cire shi daga shugabancin APC, a kan cewa bai cancanci naɗin da aka yi masa ba.

Su na jayayyar cewa haƙƙin ‘yan yankin Arewa ta Tsakiya ne aka bai wa Ganduje, ɗan yankin Arewa maso Yamma.

People are also reading