Home Back

Bankuna Sun Fara Ƙin Karɓar Yagaggun Takardun Naira, CBN Ya Shirya Ɗaukar Mataki

legit.ng 3 days ago
  • Babban bankin Najeriya (CBN) ya ce ya samu korafe-korafe masu yawa kan bankuna ba sa karbar lalatattun takardun Naira
  • Bankin CBN ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen sanya takunkumi mai tsauri kan bankunan da aka kama suna kin karbar kudin
  • CBN ya tunatar da bankuna cewa har yanzu dokarsa mai lamba COD/DIR/GEN/CIR/01/006 ta kin karbar kudi daga jama'a tana aiki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya yi barazanar ladabtar da bankunan ajiyar kudi (DMBs) da suka ki amincewa da karbar lalatattun takardun Naira daga abokan huldarsu.

Wata sanarwa dauke da sa hannun Solaja Olayemi, mukaddashin daraktan sashen hada-hadar kudi na CBN, ta ce korafe-korafe sun fara kan bankunan.

CBN ya yi magana kan bankunan da ke kin karbar lalatattun takardun Naira
CBN ya ce zai hukunta bankunan da ke kin karbar lalatattun takardun Naira. Hoto: @cenbank/X, Apajukun/Facebook Asali: UGC

Lalatattun kudi: CBN zai hukunta bankuna

A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis a shafinsa na intanet, CBN ya yi barazanar zartar da hukunci mai tsauri kan duk wani banki da ya ke kin karbar yagaggun kudaden.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Babban Bankin Najeriya (CBN) ya samu rahotanni da dama na kin karbar lalatattun takardun kudin Naira da wasu bankunan DMBs suke yi.
“Saboda haka, ana tunatar da bankuna cewa dokar CBN mai lamba COD/DIR/GEN/CIR/01/006, wadda ta tanadi hukunci kan bankuna masu kin karbar takardun Naira, har yanzu tana aiki."

Babban bankin ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen sanya takunkumi mai tsauri kan bankunan da aka kama sun ki karbar lalatattun takardun Naira daga jama’a.

CBN ya gargadi 'yan canjin Najeriya

Har ila yau, a ranar 2 ga watan Yuli, CBN ya gargadi bankuna da 'yan canji kudin kasashen waje da ke kin karbar tsofaffin takardun Dala da masu gajerun takarda.

Babban bankin ya ce dole ne dukkanin bangarorin da abin ya shafa su bi wannan umarnin, yana mai jaddada rashin goyon bayansa kan kin karbar lalatattun kudin.

CBN ya kwace lasisin bankin Heritage

A wani labarin, mun ruwaito cewa babban bankin Najeriya CBN ya kwace lasisin bankin Heritage Plc saboda ya karya sashe na 12 (1) na dokar BOFIA 2020.

An ce dokar BOFIA 2020 ta na kiyaye tsarin tafiyar da hada-hadar kudi a tsakanin bankuna da sauran cbiyoyin kuɗi na kasar wanda bankin Heritage ya gaza cikawa.

Asali: Legit.ng

People are also reading