Home Back

Jami’an mu ku gujewa karɓar cin hanci da rashawa yayin aiki – Immigration

dalafmkano.com 3 days ago

Shugabar hukumar da ke kula da shige da fice ta kasa Immigration, Kemi Nanna Nandap, ta bukaci jami’ansu da su kaucewa karbar cin hanci da Rashawa a iyakokin kasa, tare da aiki tuƙuru yayin da suke gudanar da ayyukansu a iyakokin Najeriya.

Shugabar Kemi Nanna, da ta samu wakilcin HK Usman, yayin taron da hukumar kula da shige da ficen reshen jihar Kano Immigration, ta gudanar yau a hedikwatar ta, inda ta kaddamar da yaki da cin hanci da rashawa a tsakanin jami’an hukumar da kuma al’umma.

Ta kuma ce kaddamar da al’amarin zai taimaka wajen daƙile cin hanci da
rashawa a tsakanin jami’an su da kuma al’umma musamman ma a iyakokin kasar nan da kuma ofisoshin da suke aiki.

“Nasan mu masu tsaron ƙasa ne musamman ma a iyakokin ƙasa, dole ne mu yi abinda ya kamata wajen daƙile cin hanci da rashawa a cikin aikin mu: kuma jami’an mu idan suka yi aiki tuƙuru za’a samu nasara, “in ji shi”.

Da yake nasa jawabin shugaban hukumar kula da shige da fice Immigration, ta kasa reshen jihar Kano, Ibrahim Muhammad Abubakar, ya ce sun shirya taron ne domin ƙaddamar da kawar da cin hanci da rashawa a cikin aikin nasu, kasancewar ba abu ne mai kyau ba.

Ya kuma nemi goyon bayan al’ummar ƙasar nan wajen magance harkokin cin hanci da rashawa, musamman ma tsakanin su da jami’an hukumar.

Wakilin Dala FM Kano, Hassan Mamuda Ya’u ya ruwaito cewa taron ya samu halartar jami’an hukumar da dama ciki har na birnin tarayya Abuja, da kuma jami’an tsaro, kuma ciki har da jami’an hukumar kula da gidan gyaran hali na jihar Kano, da na rundunar tsaro ta Civil Defense, da kuma hukumomin gwamnati da dai sauran su.

People are also reading