Home Back

Kotu za ta yanke hukunci kan sabuwar dokar masarautun Kano da ta rushe sarakuna biyar

bbc.com 2024/9/28
..

Asalin hoton, Mai Katanga/Facebook

A yau Alhamis ne ake sa ran wata babbar kotun tarayya a Kano za ta yanke hukunci kan halasci ko akasin haka na sabuwar dokar masarautun Kano ta 2024 wadda ta rushe sarakuna biyar na Kano da Rano da Ƙaraye da Gaya da kuma Bichi.

A watan Mayun da ya gabata ne dai 'yan majalisar dokokin jihar ta Kano suka yi ƙudirin dokar inda kuma ba tare daɓata lokaci ba gwamnan Kano Abba kabiru Yusuf ya sama ta hannu ta zama doka.

Bisa dokar ne gwamnan ya rushe sarakunan biyar ciki har da Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma sake naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin sarki na 16, bayan da tsohon gwaman jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya tuɓe a 2020.

To sai da kuma a ranar 23 ga watan na Mayu ne ɗaya daga cikin masu naɗa sarkin Kano, Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi mai sarautar Sarkin Dawaki Babba ya ƙalubalanci dokar a babbar kotun tarayyar da ke Kano, inda ya nemi alƙalin da ya rushe dokar a matsayin haramtacciya.

Kuma bayan sauraren ƙorafin mai ƙara, Mai Shari'a Abdullahi Liman ya ɗage ƙarar zuwa yau Alhamis domin yanke hukunci kan buƙatar mai ƙarar.

People are also reading