Home Back

Ana Tsaka da Wahalar Fetur, NNPCL Ya Fadi Abin da Ya Jawo Dogon Layi a Gidajen Ma

legit.ng 2024/7/23
  • Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL, ya sanar da dalilan da suka kawo matsalar karancin man fetur da ake fuskanta a sassan kasar
  • NNPCL ya ce an samu dogon layi a gidajen mai ne sakamakon ruwan sama da ake yi da ya hana kaiwa gidajen mai fetur a kan lokaci
  • Ambaliyar ruwa da ake fama da ita a babban birnin tarayya da wasu jihohi ya taimaka wurin rashin mai a gidajen mai, inji NNPCL

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kamfanin man fetrur na Najeriya, NNPCL, ya ce akwai dalili ganin jerin gwanon layin motoci a gidajen man babban birnin tarayya da wasu sassan kasar nan.

Kamfanin NNPCL ya ce an samu karancin fetur a gidajen man ne sakamakon tsaikon da aka samu wajen yin juyen man fetur daga jirgin ruwa zuwa wani jirgin.

NNPCL ya yi magana kan wahalar fetur da ake fuskanta a Najeriya.
NNPCL ya jero abubuwan da suka assasa layikan siyan man fetur a Najeriya. Hoto: NNPLC, Getty Images Asali: Getty Images

NNPCL ya yi magana kan wahalar fetur

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, an kuma samu tsaiko wajen sauke mai daga babbar gangar ajiyar man zuwa kanana sakamakon tsawa da ruwa mai karfi da aka rika yi a baya-bayan nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata sanarwa da da kamfanin NNPCL ya fitar, yace matsalar yanayi ya shafi dorawa motocin dakon mai fetur din da kuma jigilarsa zuwa gidajen mai.

Sanarwar ta ce hukumar NIMET ta shawarce shi kan yin taka tsantsan wajen loda fetur din yayin da ake ruwan sama tare da tsawa, kamar yadda AIT ya ruwaito.

Matakin da NNPCL ya dauka

Kamfanin NNPCL ya ce matsalar ambaliyar ruwa a hanyoyin manyan motoci ya haifar da wannan matsalar ta rashin man a fadin babban birnin tarayya.

Ya tabbatar da cewa, yana aiki tare da masu ruwa da tsaki wurin shawo kan matsalar sufurin tare da samar da man fetur ga yankunan da abin ya shafa.

NNPCL ya ce tuni aka fara loda man domin kai shi yankunan da wadannan matsalolin suka ragu, inda ya ce nan gaba kadan matsalar za ta zama tarihi, inji rahoton Tribune.

Rashin man fetur ya tsananta a Abuja

A wani labari na daban, mun ruwaito cewa jerin layin ababen hawa a gidajen mai ya tsananta a cikin birnin Abuja wanda ake alakanta hakan da rashin man fetur a gidajen man.

A yankunan Wuse da Jabi da ke cikin Abuja, an ga wasu gidajen man a rufe yayin da wasu ke bude amma babu man kwata-kwata.

Asali: Legit.ng

People are also reading