Home Back

HARIN ABUJA: ‘Kafin ƴan ta’adda su fara kwashe mutane na ankare, na kauce na kama gana na – wani Mazauni

premiumtimesng.com 2024/9/27
HARIN ABUJA: ‘Kafin ƴan ta’adda su fara kwashe mutane na ankare, na kauce na kama gana na – wani Mazauni

Wasu daga cikin mazauna unguwar Dawaki da ƴan bindiga suka afka wa suka sace mutane ya bada labarin yadda ya yi wa ƴan bindiga layar zana ya arce ba su haɗa da shi ba.

Mazaunin unguwar ya ce, yana zaune sai ya gansu sun shigo duk fuskokin su a rufe da zani.

” Da na gansu taye sun doso mu sai na tambayi wasu masu kitso cewa yaushe aka fara makarantar Islamiyya na mata a unguwar nan don naga wasu da hijabi sa ban saba ganin su ba.

“Daga nan sai na ja baki na na yi shiru ta shi baki na alaikum na ce musu bari in dan shiga baya can in yi bahaya, daga nan sai na sulale.

Wata mata da ta tsallake rijiya da baya, ita ma ta kubuta daga hannun ƴan bindigan ta bayyana cewa bayan an tattara su an nausa da su saman duwatsu, jami’an tsaro sun biyo su a lokacin da aka yi arangama ne ta samu ta arce tare da wasu.

Sai dai kuma ba kamar yadda ƴan sanda suka rika faɗi ba cewa wai sun ceto duka wanda aka yi garkuwa da, shugaban mazauna rukunin gidaje na Dawaki a ranar Talata ya shaida cewa akwai wasu da dama da ke tsare hannun ƴan bindigan har yanzu.

Yabi gida-gida ya na tambayar mazauna ko mutum nawa ke na su da ke hannun ƴan bindiga, su kuma suna faɗi.

Jami’an tsaro sun yi ikirarin cewa ba za su yi kasa a guiwa ba wajen ganin sun ceto wadanda ke tsare hannun ƴan bindigan.

People are also reading