Home Back

Ku guji zubar da Shara barkatai a muhallan ku – Gwamnatin Kano

dalafmkano.com 2024/5/19

Gwamnatin jihar Kano ta gargadi al’umma da su kaucewa zubar da shara a wuraren da ba’a tanade su ba, domin kaucewa yawaitar samun cutuka a tsakanin al’umma, duba da yadda ake ci gaba da tunkarar lokacin Damuna.

Shugaban hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar Kano Ambasada Ahmadu Haruna Zago, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake sanya ido kan aikin kwashe sharar da ke unguwar Zango hauran gadagi bayan Festival.

Ya ce duba da yadda Damuna ke ci gaba da tunkarowa, akwai bukatar al’umma su fahimci cewa zubar da shara barkatai ka iya haifar da cututtuka daban-daban ga iyalan su, musamman ma kasancewar sharar da ke unguwar ta Zango bayan Festival, tana tsakiyar gidajen al’umma ne da kasuwa da kuma makaranta.

Nazifi Mohammed Usman mai Duniya, da Mohammed Ibrahim wato Halifa mai Gas mazauna unguwar ta Zango ne, sun ce tarin sharar a cikin unguwar su babban ƙalubale ne a gare su, domin kuwa taruwar da tayi har ta kan shiga cikin makarantar yankin su.

Shugaban hukumar kwashe sharar Ahmadu Zago, ya kuma sha alwashin yin duk mai yiwuwa wajen tsafta ce birnin Kano, wajen kwashe shara daga kowane yankin, domin gudun faruwar ambaliyar ruwa sanadin sharar da ka toshe magunan ruwa a jihar Kano.

People are also reading