Home Back

Gwamna Abba Ya Rantsar da Mustapha Kwankwaso da Wasu Kwamishinoni 3

legit.ng 2024/5/15
  • Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso ɗan tsohon gwamnan jihar Kano ya samu muƙamin kwamishina a gwamnatin jihar Kano
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da Mustapha tare da wasu mutum uku a matsayin sababbin kwamishinoni a gwamnatinsa
  • Mustapha zai jagoranci ma'aikatar matasa da wasanni yayin da sauran mutum uku su ma aka ba su ma'aikatun da za su jagoranta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da sababbin kwamishinoni huɗu a gwamnatinsa.

Daga cikin sababbin kwamishinonin da aka rantsar akwai Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ɗa ne a wajen jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso.

An rantsar Mustapha Kwankwaso
Mustapha Kwankwaso ya zama kwamishinan matasa na Kano Hoto: @Kyusufabba/@imranvashyr Asali: Twitter

Kwamishinonin waɗanda aka rantsar a ranar Alhamis, 18 ga watan Afirilun 2024 an kuma ba su ma'aikatun da za su jagoranta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Ibrahim Adam, shi ne ya sanya batun rantsar da kwamishinonin a shafinsa na Facebook.

Sababbin kwamishinonin da aka rantsar sun haɗa da Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso, Abduljabbar Garko, Shehu Aliyu Yarmedi da Adamu Aliyu Kibiya.

Rantsar da su da aka yi domin kama aiki na zuwa biyo bayan amincewar da majalisar dokokin jihar ta yi da naɗin da aka yi musu bayan ta tantance su.

Waɗanne ma'aikatu za su jagoranta?

Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso ya zama sabon kwamishinan wasanni da matasa na jihar Kano.

Ga jerin sauran kwamishinonin da ma'aikatun da za su jagoranta:

1. Abduljabbar Garko - ƙasa da safiyo

2. Shehu Aliyu Yarmedi - ayyuka na musamman

3. Adamu Aliyu Kibiya - kasuwanci da masana’antu

An tura sunan Mustapha zuwa majalisa

A baya Legit Hausa ta kawo rahoto cewa gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya sake tura sunayen mutane huɗu majalisar dokokin jihar domin tantance su.

Mai girma Abba Yusuf ya tura sunayen zuwa majalisar ne domin tantance su a matsayin ƙarin kwamishinoni a jihar.

Ɓatun naɗa ɗan Kwankwaso kwamishina

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ce ya naɗa Mustapha ɗan Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin kwamishina saboda ya cancanta.

Gwamna Abba ya bayyana cewa Mustapha Kwakwanso yana daga cikin haziƙan matasan da suka yi aiki tuƙuru domin samun nasarar kafa gwamnatinsa a Kano.

Asali: Legit.ng

People are also reading