Home Back

Mutane Sun Shiga Fargaba Sakamakon Tashin Abin Fashewa a Gonar Sojojin Najeriya

legit.ng 2024/5/9
  • Mutane a Legas sun shiga tsananin fargaba a ranar Litinin sakamakon tashin wani abin fashewa a gonar sojoji da ke Ikeja
  • Rundunar sojoji wacce ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce "lamarin bai munana ba" yayin da ta fara gudanar da bincike kan tashin bam din
  • Ba wannan ne karo na farko da irin hakan ta faru ba inda a baya tashin bam a barikin ya yi ajalin mutane daga dama da lalata gidaje

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ikeja, jihar Legas - A ranar Litinin ne fargaba ta mamaye mazauna Legas biyo bayan tashin wani abin fashewa da ake tsammani bam ne a barikin sojoji na Ikeja da ke jihar.

Rundunar sojojin Najeriya ta yi magana kan abin fashewa da ya tashi a Legas
Sojoji sun fara bincike kan abin fashewa da ya tashi a barikinsu na Legas. Hoto: @HQNigerianArmy Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta tattaro cewa abin fashewar ya tashi ne a wata gona da ke cikin barikin.

Tashin abin fashewa a barikin sojoji

Idan ba a manta ba a ranar 27 ga watan Junairun 2002, wani abin fashewa ya tashi a barikin wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da lalata gidaje da yawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakanan a cikin Oktoba 2023, sojoji sun gano bama-bamai 642 da basu kai ga fashe wa ba a gonakin da ke cikin barikin.

Da take tabbatar da fashewar bam din a ranar litinin, jaridar Daily Trust ta ruwaito rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa lamarin bai munana.

Rundunar sojoji ta yi karin haske

Manjo Janar Onyema Nwachukwu, kakakin rundunar sojin a wata sanarwa ya ce tawagar da ke lalata ababen fashewa suna kan gudanar da bincike a wurin da abin faru.

Talabijin na Channels ya rahoto sanarwar ta kara da cewa:

“Ana zargin abin fashewar ya tashi ne sakamakon kona shara da wani manomi ya yi a gonar da aka bashi yake noma a ciki.
“An yi sa’a, ba a sami asarar rai ba a lamarin. Duk da haka, muna amfani da wannan damar wajen kwantar da hankulan mazauna wannan yankin, kuma tuni mun fara yin bincike."

Abin fashewa ya tashi a Legas

A wani labarin makamancin wannan, Legit Hausa ta ruwaito cewa wani abin fashewa ya tashi a yankin Iju Ishaga da ke jihar Legas.

A cewar hukumar ba da agajin gaggawa (NEMA) ta jihar, ta ce iskar gas ce ta fashe a wani shago dake cikin kasuwar, wanda ya jawo asarar dukiya mai yawa da jikkata mutane.

Asali: Legit.ng

People are also reading