Home Back

Shugaba Bola Tinubu Ya Naɗa Sanata Bashir Lado Mai Ba Shi Shawara

leadership.ng 2024/8/24
Shugaba Bola Tinubu Ya Naɗa Sanata Bashir Lado Mai Ba Shi Shawara

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya naɗa Sanata Bashir Lado Mohammed a matsayin Mai ba Shugaban ƙasa shawara kan harkokin majalisar dattawa. Kakakin Shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya sanar da hakan a yau Asabar.

Sanata Mohammed, ɗan siyasa ne kuma ɗan kasuwa mai kwarewa daga Jihar Kano, yana da tarihin aik a wurare da dama, inda ya taba zama Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya da kuma babban darakta na hukumar hana safarar Mutane (NAPTIP).

Shugaba Tinubu ya nuna tabbacin cewa gogewarsa mai zurfi za ta inganta haɗin kai tsakanin ɓangaren zartarwa da majalisa, wanda zai haɓaka aikace-aikacen gwamnati.

People are also reading