Home Back

Gwamnatin Tarayya Ta Fara Gina Gidaje Masu Saukin Kudi 1,250 A Jihohi Hudu

leadership.ng 2024/7/1
nijeriya

Gwamnatin tarayya ta bakin ma’aikatar gidaje da raya birane, ta sanar da fara aikin gina gidaje masu saukin kudi fiye da 1,250 a jihohi hudu na arewacin Nijeriya a tsarin da aka yi wa lakabi da ‘Renewed Hope Cities’.
A ranar Laraba ta wannan makon aka shirya kaddamar da shirin a jihar Katsina daga nan kuma za a zarce Jihar Gonmbe inda nan ma za a kaddamar da aikin gina gidajen a ranar 25 ga watan Mayu 2024.

Ministan gidaje da raya birane, Alhaji Ahmed Dangiwa ya bayyana haka a takardar sanarwar da ya raba wa manema labarai, ya ce tuni aka kammala dukakn yarjejeniyar kwangilar tare da bayar da kudin somin tabi ga dukkan ‘yan kwangilar da suka samu aikin gina gidajen a fadin arewacin Nijeriya.

Shirin ya biyo bayan kaddamarwa da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya yi ne na gina gidaje 3,112 a unguwar Karsana da ke babban birnin tarayya, Abuja a watnb Fabrairu na shekarar 2024.

Sanarwar wanda da jami’in watsa labarai na ministan, Mark Chieshe, ya sanya wa hannu ya kuma jaddada aniyar gwamnatin Tinubu na samar da gidaje masu saukin kudi a fadin kasar nan tare da kuma samar wa matasanmu aikin yi wanda hakan zai bunkasa tattalin arzikin kasa.

Sanarwa ta kuma ce, “Ministan zai kaddamar da fara aikin gina gidajen kamar haka, gidaje 250 a Katsina a ranar Laraba 22 ga watan Mayu, 2024, sai gidaje 500 a garin Kano a ranar Alhamis 23 ga watan Mayu 2024 sai kuma gidaje 250 a Jihar Yobe a ranar Juma’a 24 ga watan Mayu 2024, daga nan kuma sai Jihar Gombe inda za a gina gidaje 250 a ranar 25 ga watan Mayu. Dukkan gidajen an yi musu lakabi da ‘Renewed Hope Estate’.

“Mun tsayu na ganin cika alkawarin da Shugaban Kasa Tinubu ya yi wa ‘yan Nijeriya na mayar da fadin kasar nan fagen gine gine, ta nan kuma muna sa ran a samar wa matasa aikin yi.,” in ji MInistan

Ya kuma kara da cewa, zuwa yanzu ma’aikatar ta bayar da kwangilar gina gidaje fiye da 3,500 a jihohi 13 na kasar nan tun daga watan Disamba na shekarar 2023 a karkashin kasafin kudin kasa da aka gabatar na cike gurbi.

Jihohin sun kuma hada da Katsina, Sokoto, Yobe, Gombe, Nasarawa, Benue, Osun, Oyo, Abia, Ebonyi, Delta da Akwa Ibom.

People are also reading