Home Back

Kwalejin Koyon Tuƙin Jirgi ba ta da jirgin koyon tuƙi ko ɗaya – Shugaban Kwajeli

premiumtimesng.com 2024/4/30
Kwalejin Koyon Tuƙin Jirgi ba ta da jirgin koyon tuƙi ko ɗaya – Shugaban Kwajeli

Majalisar Tarayya ta sha alwashin cewa sai ta ƙwato jiragen sama biyu ƙirar Bell 206L4 BZB da kuma Bell M2062-L4, waɗanda mallakar Kwalejin Koyon Tuƙin Jirage ne (NCAT) da ke Zariya, amma aka sayar da su ga wasu shafaffu da mai.

Shugaban Kwamitin Bin Diddigin Kadarorin Gwamnati, Ademoyin Kuye ne ya bayyana haka, a lokacin zaman binciken da kwamitin ya yi, inda ya saurari bayanin yadda aka sayar da jiragen biyu.

An yi zaman kwamitin sauraren sabarƙalar a Majalisar Tarayya, ranar Alhamis, a Abuja.

Kuye ya bayyana cewa abin damuwa ne matuƙa jin yadda aka sayar da jiragen ga wasu mutane, lamarin da ya sa kwalejin ta kasance ba ta da sauran jiragen koyon tuƙi ko ɗaya.

Haka kuma kwamitin ya tambayi yadda aka yi har aka sayar da jiragen biyu ga wasu mutane daban, alhali kuma Rundunar Sojojin Saman Najeriya, Rundunar Sojojin Ruwa da kuma Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya duk sun nuna buƙatar saye, amma aka ƙi sayar masu, aka saida wa wasu mutum biyu daban.

Binciken ya nuna cewa mahukuntan kwalejin ne suka ƙi sayar wa jami’an tsaro jiragen.

Majalisar Tarayya ta gano cewa ɓangarorin jami’an tsaro ukun da suka rubuta takardar neman a sayar masu da jiragen, sun kuwa tura tawaga har cikin kwalejin domin gane wa idanun su yadda jiragen suke, amma duk da haka aka ƙi sayar wa wasu daban.

Shugaban Riƙo na Kwalejin Koyon Tuƙin Jirage da ke Zariya (NCAT), Shakespeare Imalighwe, ya ce duk da a lokacin da aka sayar da jiragen ya na Mataimakin Shugaba, ba a yi shawara da shi ba wajen sayarwar, ƙarshe ba a ma saka shi cikin ‘yan kwamitin sayar da jiragen ba.

Ya ce ya karɓi kwalejin a matsayin Shugaban Riƙo cikin Janairu, 2024.

Ya shaida wa kwamitin cewa jiragen lafiya ƙalau suke a lokacin da aka sayar da su. Kuma a a lokacin akwai kamfanin da ke kula wajen yi wa jiragen garambawul kafin a sayar da su.

Daga nan ya shaida masu cewa a zaman yanzu dai babu jirgin koyon tuƙi a kwalejin ko ɗaya.

Daga nan kwamiti ya umarci tsohon Ministan Sufuri Hadi Sirika da Ministan Sufurin Jiragen Sama na yanzu, Festus Keyamo su bayyana gaban kwamitin.

 
People are also reading