Home Back

"Zan biya N200,000": Bobrisky Ya Saukar da Kai, Ya Nemi Alfarma Kan Hukuncin Kotu

legit.ng 2024/5/4
  • Yayin da aka daure shi har na tsawon watanni shida, ɗan daudu Idris Okuneye ya nemi alfarma kan hukuncin kotun
  • Bobrisky ya bukaci kotun ta yi masa sassauci wurin sauya zaman gidan kaso zuwa kudi N200,000 domin ya biya
  • Wannan na zuwa ne bayan alkalin kotun a jihar Legas, Abimbola Awogboro ya yanke masa hukunci kan cin mutuncin naira

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Fitaccen ɗan daudu a Najeriya, Idris Okuneye ya roki alfarma kan hukuncin da aka yanke masa a Legas.

Ɗan daudun da aka fi sani da Bobrisky ya roki alfarmar a sauya masa zaman gidan yarin zuwa tsurar kudi domin ya biya.

Bobrisky ya roki alkalin kotun da ya yanke masa hukunci
Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky ya bukaci biyan N200,000 kan laifuffukansa. Hoto: @Bobrisky222. Asali: Instagram

Wace alfarma Bobrisky ya nema a kotu?

Lauyan ɗan daudun, Bimbo Kusanu shi ya yi wannan roko inda ya bukaci mayar da laifuffukan kowane guda daya N50,000, cewar BusinessDay.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauya ya bukaci hakan ne domin Bobrisky ya biya N200,000 kan dukkan korafe-korafen da ke yi kansa domin samun sauƙi.

Wannan ya biyo bayan daure Bobrisky da alkalin kotun, Abimbola Awogboro ya yi na tsawon watanni shida ba tare da biyan tara ba.

An yanke masa wannan hukunci ne kan zargin cin zarafin naira da kuma wulakanta ta da ya yi wanda ya amsa laifinsa.

Karin bayani na tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading