Home Back

Ban sauya matsaya kan cire tallafin man fetur ba - Tinubu

bbc.com 2024/10/6
Shugaban Najeriya Bola Tinubu

Asalin hoton, fb/Bola Tinubu

Gwamnatin Najeriya ta ce har yanzu ba ta sauya matsayarta ba game da cire tallafin man fetur, kamar yadda shugaban ƙasar ya sanar a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labaru, Bayo Onanuga, ta bayyana cewa: “Gwamnati na son jaddada cewa matsayarta kan cire tallafin man fetur ba ta sauya ba daga abin da shugaba Bola Tinubu ya bayyana a ranar 29 ga watan Mayu, 2023”

“Zamanin tallafin man fetur ya ƙare.

“Ba a ware naira tiriliyan 5.4 kan tallafin man fetur ba a kasafin kuɗin 2024, kamar yadda ake ta raɗe-raɗi a kai”.

Wannan sanarwa na zuwa ne bayan da wasu mkafafen yaɗa labaru suka bayyana cewa Najeriya na ci gaba da biyan kuɗin tallafin man fetur ta ƙarƙashin ƙasa.

Labarin ya ce wasu bayanai da aka samu sun nuna cewa gwamnati ta ware kuɗi sama da waɗanda aka ware domin biyan tallafin man fetur a shekarar 2023.

Sai dai sanarwar da gwamnatin ta fitar a yau Alhamis ta ce bayanin da ake ta maganganu a kai wasu shawarwari ne kawai kan tsare-tsaren kuɗi da aka gabatar wa shugaban ƙasa domin yin nazari.

Waɗannen shawarwari ne suka janyo ruɗani?

Tun farko dai bayanai sun nuna cewa akwai yiwuwar Najeriya ta kashe kuɗi har naira tiriliyan 5.4 a shekarar 2024 kan tallafin man fetur, wanda hakan ya nunka abin da ƙasar ta kashe a 2023 kan tallafin na man fetur.

Sannan gwamnatin Najeriyar za ta ranto ƙarin kuɗi naira tiriliyan 6.6 domin cike giɓin kasafin kuɗin ƙasar – in ji kamfani dillancin labaru na Reuters.

Shawarwarin da aka miƙa wa shugaban ƙasar kan tsarin daidaitawa da bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa wanda aka yi wa take ‘Accelerated Stabilisation and Advancement Plan’ a turance – wanda ma’aikatar kuɗi tare da ɓangaren ƴan kasuwa suka rubuta, na da manufar magance ƙalubalen da suka shafi sauye-sauyen da gwamnati ta kawo domin bunƙasa ci gaban ƙasa.

A watan Mayun 2023 ne shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya soke tallafin man fetur, wani mataki da masu zuba jari suka jinjina mawa.

Sai dai hakan ya jefa al’ummar ƙasar cikin mawuyacin hali, inda farashin sufuri da na kayan masarufi ya yi tashin gwauron zabi.

Tun daga wancan lokacin Tinubu ke fuskantar matsi daga al’umma da ƙungiyoyin ƙwadago.

Haka nan an riƙa raɗe-raɗin cewa gwamnatin na biyan tallafin man fetur ɗin a ɓoye, sai dai ta musanta hakan.

Wani abu da ya haifar da tababa kan iƙirarin gwamnatin Najeriyar kan cire tallafin man fetur shi ne yadda farashin litar man fetur bai sauya ba tun cikin watan Yulin 2023, duk kuwa da cewa an saukar da darajar naira sau biyu a hukumance.

Wani ɓangare na shawarwarin da ma'aikatar kuɗin ta gabatar wa Tinubu na cewa: "A farashin da ake yanzu, akwai hasashen cewa abin da za a kashe kan tallafin man fetur zai kai naira tiriliyan 5.4 nan da ƙarshen 2024. Wannan ya zarce abin da aka kashe - naira tiriliyan 3.6 a 2023 da kuma naira tiriliyan 2.0 a 2022".

People are also reading