Home Back

Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Fitar Da Dala Miliyan Biyar Daga Asusun IFAD Don Bunkasa Noma

leadership.ng 2024/5/18
Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Fitar Da Dala Miliyan Biyar Daga Asusun IFAD Don Bunkasa Noma

Gwamnatin Tarayya ta hanyar Ma’aikatar Aikin Noma da Samar da Abinci, ta bukaci a fitar da dala miliyan biyar a asusun bayar da tallafin bunkasa aikin noma na kasa da kasa (IFAD) domin wanzar da aikin tallafa wa iyalai a yankin Neja Delta (LIFE-ND), da kuma shirin habaka noma domin samun gwaggwabar riba (BCDP).

Ministan Ma’aikatar Abubakar Kyari ne ya yi wannan kira a lokacin da ya karbi bakuncin Mataimakin Shugaban IFAD, Donal Brown a Abuja.

A cewar Kyari, gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen ci gaban IFAD, musamman domin ciyar da fannin kimiyyar aikin noma a fadin wannan kasa.

Ya ce, “Na yi ammana da cewa, wasu daga cikin matakan da aka dauka na wanzar da aikin na LIFE-ND; wadanda suka hada da amincewa da bukatar fadada shirin a cikin shekara daya, karin bukata ta dala miliyan 20, don fara wannan shiri na LIFE-ND zuwa kashi na biyu”.

A cewarsa,“An tsara shirin ne bisa nufin jawo kungiyoyin hadaka daban daban da kuma kwarru masu ruwa da tsaki wadanda za su wakilici al’ummar gari da masu zaman kansu da sauran makamantansu, domin yin amfani da fasahar zamani don kara habaka wannan fanni na aikin noma da kuma kara karfafa gwiwar kananan manoma.”

A nasa jwabin, Donal Brown ya sanar da cewa; burin da IFAD ke son cimma; ba wai ya tsaya ne kawai wajen karfafa dangantaka ba, har ma da yadda IFAD din za ta yi duba a kan makomar taimakawa gwamnatin wannan kasa.

Haka zalila, ya bayyana cewa; “IFAD zai bayar da gagarumar gudunmawa wajen taimaka wa gwamnati, musamman don kara samar da wadataccen abinci a fadin wannan kasa baki-daya”.

People are also reading