Home Back

Takaitacciyar tsagaita wuta za ta fara aiki a Gaza

dw.com 2024/9/27
Wasu a yankin Rafah na kudancin Gaza
Wasu a yankin Rafah na kudancin Gaza

Akwai dai dubban daruruwan Falasdinawa da ke cikin hali na neman jinkai a musamman yankin Rafah da ke kudancin Gazar a yanzu, bayan tashin wutar yaki a tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas da ya shiga watanni tara a yanzu.

Yankin da matakin tsagaita wutar a takaice zai shafa, yanki ne mai fadin kilomita 12 a kan hanyar da ta shafi yankin na Rafah, abin da ake ganin ya yi karanci matuka.

Kasashen duniya ne dai suka bukaci hakan ciki har da Amurka da ke babbar kawar Isra'ila.

Dakarun Isra'ila dai sun ce takaitacciyar tsagaita wutar ta kullum za ta fara ne daga karfe takwas na safiya zuwa bakwai na yammaci agogon Gazar, ba tare da kayyade tsawon lokaci ba.

People are also reading