Home Back

‘Yan ta’adda 176 Sun Mika Wuya, An Cafke 57 A Tafkin Chadi – MNJTF

leadership.ng 2024/6/30
‘Yan ta’adda 176 Sun Mika Wuya, An Cafke 57 A Tafkin Chadi – MNJTF

Rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa (MNJTF) ta sanar da cewa, mayakan kungiyar Boko Haram 176 ne suka mika wuya, yayin da aka cafke wasu 57 da ake zargin suna da hannu a ayyukan ta’addanci a yankin tafkin Chad.

Kwamandan rundunar, MNJTF “Operation Lake Sanity II,” Maj.-Gen. Ibrahim Ali ya bayyana hakan a ranar Talata yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a barikin rundunar hadin gwiwa “JTF Operation Hadin Kai” da ke unguwar Maimalari da ke Maiduguri.

Maj.-Gen. Ali ya ce, an samu wannan nasarar ce sakamakon wani gagarumin aiki na share ragowar ‘yan ta’adda da ke yankin tafkin Chadi a ranar 23 ga Afrilu, 2023.

Kwamandan rundunar ya kuma kara da cewa, farmakin na hadin gwiwa ya hada da sojoji daga kasashen Kamaru, Chadi, da jamhuriyar Nijar wadanda suka fatattaki wasu muhimman guraren ‘yan ta’adda a yankin tafkin Chadi da suka hada da Doron Naira, Zanari, da Bagadaza.

People are also reading