Allahu Akbar: An Yi Jana’izar Mahaifin Sanatan Arewa, Shettima da Sanatoci Sun Halarta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa jana'izar Alhaji Tijjani Muhammad, mahaifin sanatan Borno ta Arewa, Mohammed Tahir Munguno.
An ruwaito cewa marigayi Alhaji Muhammad, ya rasu ne a daren ranar Asabar a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri bayan doguwar jinya, yana da shekaru 95.
Kamar yadda Kashim Shettima ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, babban limamin Borno, Mamman Shettima Saleh ne ya jagoranci Sallar jana'izar a tsohon gidan Sanata Munguno.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin wadanda suka halarci jana'izar akwai mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, Sanata Ali Ndume da ministan noma, Abubakar Kyari.
Sauran sun hada da ministan cikin gida kan ci gaba ƙarafa, Uba Maigari Ahmadu, mukaddashin gwamnan Borno, Dr. Usman Kadafur da dai sauran su.
Duba hotunan jana'izar da ta'aziyyar a nan ƙasa:
Sanata Barau Jibrin, ya wallafa a shafinsa na X cewa:
"InnalilLahi wa inna ilaihi raji'un.
"A yau na kasance a Maiduguri, babban birnin jihar Borno inda na halarci jana'izar Alhaji Tijjani Muhammad, mahaifin abokinmu, Sanata Tahir Munguno."
Kalli saƙon sanatan a nan ƙasa:
Tun da fari, wani ma'abocin shafin Facebook, Muhammad Umar B. Ali ne ya sanar da rasuwar Alhaji Tijjani Muhammad a jiya Asabar, 22 ga watan Yuni.
Umar B. Ali ya ce Alhaji Tijjani ya kasance ɗan kasuwa na ƙasa da ƙasa, wanda ya kasance mutumin ƙwarai, abin koyi ga jama'a.
Ya ce Alhaji Tijjani ya rasu ya bar ƴaƴa 17, ciki har da Sanata Munguno, da Injiniya Usman, shugaban kungiyar injiniyoyi ta Borno, da Barista Ibrahim, wanda ya assasa cambar lauyoyi ta Munguno, da dai sauran su.
Asali: Legit.ng