Home Back

Jirgin Najeriya: Ana tsaka da taƙaddama a Kano, ministan Tinubu ya dakatar da aikin Buhari

legit.ng 2024/7/3
  • Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya jaddada cewa gwamnati ta dakatar da aikin jirgin saman Najeriya sai baba ta gani
  • Tun farko dai tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya kaddama da jirgin Nigeria Air kwanaki uku kafin ya sauka daga mulki
  • Amma bayan gano wasu kura-kurai, Gwamnatin Bola Tinibu ta dakatar da aikin a watan Agusta, 2023 ta bakin Mista Keyamo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ta ƙara jaddada cewa ta dakatar da aikin jirgin saman Najeriya.

Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ne ya bayyana haka a wurin taron manema labarai na cikar Tinubu shekara ɗaya a kan mulki a Abuja ranar Litinin.

Festus Keyamo.
Gwamnatin tarayya ta ƙara tabbatar da dakatar da aikin kamfanin jirgin saman Najeriya Hoto: Festus Keyamo Asali: Facebook

A 2023 ma’aikatar sufurin jiragen sama karkashin tsohon minista Hadi Sirika ta kaddamar da kamfanin jirgin saman Najeriya watau 'Nigeria Air'.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda The Cable ta ruwaito, an kaddamar da jirgin saman Najeriya ne kwanaki uku kafin karshen gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Lamarin dai ya ta da ƙura a fadin Najeriya musamman kan tsarin yarjejeniyar mallaka, wanda ya baiwa kamfanin jiragen saman ƙasar Habasha kashi 49%.

A watan Agusta 2023, Keyamo ya ba da sanarwar cewa an dakatar da aikin jirgin saman Najeriya wanda Buhari ya fara gab da zai bar mulki, The Nation ta ruwaito.

Gwamnatin Tinubu ta jaddada dakatarwar

Da yake ƙarin bayani a taron manema labarai na ministoci da aka yi a Abuja don murnar cikar Tinubu shekara daya a kan karagar mulki, Keyamo ya ce matakin dakatar da aikin na. nan har yanzu.

"Mun dakatar da aikin har kawo yanzu saboda maganar gaskiya ba jirgin saman Najeriya bane, kawai fentin Najeriya aka yi wa jirgin amma kamfanin jirgin ƙasar Habasha ne ke kokarin amfani da tutar mu.
"Dole kamfankn Air Nigeria ya zama na ‘yan kasa, dole ne ya zama Najeriya ce ta mallake shi, kuma ga zama wanda zai kawo ci gaban Najeriya, ba wai a tura kashi 50 na ribar ga wata kasa ba."

- In ji Keyamo.

Hadimin Ganduje ya caccaki Abba

A wani rahoton na daban hadimin shugaban APC na ƙasa ya soki Gwamna Abba Kabir Yusuf kan yunƙurin wargaza ayyukan da Ganduje ya yi a Kano.

Cif Oliver Okpala ya ce abubuwan da ke faruwa a Kano wata manaƙisa ce da aka shirya da nufin ganin bayan tsohon gwamna Ganduje.

Asali: Legit.ng

People are also reading